KORONA: A daure a ci gaba da wanke hannaye domin dakile yaduwar cutar – Hukumar NCDC

0

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta hori mutane da su daure da wanke hannaye a koda yaushe da ruwa da sabulu domin guje wa kamuwa da kuma yada cutar korona a kasa.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka a taron ranar tsaftace hannaye na duniya da aka yi a Abuja ranar Larabar makon jiya.

Ihekweazu ya ce baya ga kaucewa kamuwa da korona da wanke hannaye da ruwa da sabulu ke yi, yin haka na kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

Alfanun wanke hannaye da ruwa da sabulu

1. Koya wa yara dabi’ar wanke hannuwa da ruwa da sabulu na kare su daga kamuwa da mugan cututtuka.

2. Mafi yawan mutanen Najeriya basu wanke hannayen su da ruwa da sabulu.

3. Ya zama dole a rika wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

4. Wanke hannu da ruwa da sabulu na rage yawan mace-macen mutane.

5. Ya zama dole wa ma’aikatan kiwon lafiya su rika wanke hannayen su da ruwa da sabulu kafin da bayan sun duba marasa lafiya.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 37 da suka kamu da cutar korona ranar Lahadi.

Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihohi bakwai a kasar nan.

Wadannan jihohi sun hada da Yobe-13, Lagos-12, Akwa Ibom-6, FCT-3, Edo-1, Kaduna-1 da Ogun-1.

Hukumar ta ce babu wanda ya mutu a dalilin kamuwa da cutar a kasar nan ranar lahadi.

Zuwa yanzu mutum 165,419 ne suka kamu, mutum 7,054 na killace a asibitocin kula da masu fama da cutar.

Sannan mutum 156,300 sun warke, mutum 2,065 sun mutu a kasar nan.

Share.

game da Author