Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya kalubalanci kalaman da ministan Shari’a, Abubakar Malami yayi cewa wai hana kiwo a Fiki kamar hana saida kayan gyaean motoci ne a yankin Arewa.
Malami ya fadi haka a lokacin da yake hira da tashar talbijin din Channels a Abuja.
Malami ya ce hana kiwo a fili da wasu gwamnonin kasar nan suka yi daidai yake da a ce an daina saida da kayan gyaran motoci a jihobin Arewa.
A martani da ya maida wa minista Malami, gwamna Akeredolu ya ce koma dai menene, ba zai yarda a yi kiwo a fili ba a jihar Ondo sai dai fa idan bashi bane gwamna a jihar.
” Ba babatu Malami zai rika yi ba idan yana ganin zai iya dakatar da gwamnonin yankin kudu da suka saka wannan doka na hana kiwo a fili ya garzaya kotu mana. Ni a shiye nake mu gwabza a kotu ya gani ko zai iya nasara akan mu.
” Wadannan dokoki ne na jihohi wanda dokar kasa ta ba da dama ayi irin su. Kuma dokokin mu suka sa muka yi irin haka. Saboda haka babu wani da zai yi nadamar haka kuma doka ce yanzu da dukkan mu gwamnonin yankin kudu muka sa yi na’am da shi.