KISAN GULAK: Tir da wadanda basu kwaunar zaman lafiya a kasar nan – Buhari

0

Sbugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi tir ta wadanda suke tada zaune tsaye a kasar nan wadanda ba su kaunar zaman lafiya a kasar nan.

Buhari ya ce kisan Ahmed Gulak da wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba su ka yi ya yi matukar girgiza shi.

” Na yi matukar girgiza a lokacin da na ji labarin kisar da aka yi Ahmed Gulak wanda wasu tsirarun shaidanu da basu son zaman lafiya su ka aikata.

” Ina so in yi wa irin wadannan shaidanun mutane wadanda suka aikata kisan da ma masu aikata shaidanci irin haka cewa ba za a zuba ido a barsu suna yin abinda suka ga dama ba. Gwamnati za ta yi amfani da duk wata dama da ta ke da shi wajen ganin an bankado su an kuma hukunta su.

A karshe shugaba Buhari ya yi alhinin kisan Gulak, sannan ya yi addu’ar Allah ya ji kan sa ya muma ba iyalan sa hakuri jure rashin sa.

Kakakin fadar shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya saka hannu a sakon shugaban kasa.

Yadda ‘Yan bindiga suka kashe Ahmed Gulak a Owerri, Jihar Imo

Tsohon, Kakakin majalisar Dokokin jihar Adamawa, tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan siyasa, Ahmed Gulak ya gamu da ajalin sa a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar Asabar.

Ana zargin wasu ƴan bindiga ne suka bindige shi a hayar sa ta zuwa filin jirgi daga dakin Otel din sa a Owerri zai dawo Abuja.

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa da ma kuma akwai wani bidiyo da aka samu dake bayyana sakon shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya na gargadin duk wani mazaunin garin Owerri kada ya fita waje kwata-kwata na tsawon kwanaki biyu.

” Ban ga dalilin da zai sa gidajen jaridu da ‘yan Najeriya za su zasu rika kiran’ yan IPOB’ ‘Yan bindiga ba, bayan an san su kuma sun fadi cewa su ne ke kai wa ofishoshin’ yan sanda harere da mutanen da basu ji ba, ba su gani ba”.

Share.

game da Author