Shugaban Muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya yi wa Gwamnonin Kudu 17 wankin babban bargo bayan sun fitar da kudirori 12, wadanda a cikin su har su ka haramta kiwon shanu kuma su ka nemi a kyale jihohi su kafa ‘yan sandan su, kuma a gaggauta sauya fasalin Najeriya.
Tare da ragargazar gwamnonin, Osita ya hada gaba dayan gwamnonin Najeriya ya yi masu kwasar-karan-mahaukaciya ya watsa su cikin bola.
Ya bayyana cewa matsawar Najeriya ta yi mummunan sakacin da ta kara wa gwamnoni karfin iko, to sai kuwa an yi mummunan da-na-sani nan gaba ba da dadewa ba.
“Shin a yanzu ma wace aka cika, irin yadda gwamnoni su ka zama Fir’aunonin kan su, su na take doka yadda su ka ga dama, to ina ga an kara masu karfin iko kuma?
“In banda rashin kunya, gwamnonin nan fa tun cikin 2018 Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar cin gashin kan kotunan jihohi da Majalisar Dokokin Jihohi. Amma har yau gwamnonin Najeriya sun shafa wa idanun su toka, sun ki fara aiki da dokar.
‘Yanzu irin wadannan Fir’aunonin da ke take doka sun hana kotuna da Majalisar Dokoki cin gashin kai, su ne za su nemi a ba su dama su kafa ‘yan sandan jihohi? Ya ku ke tsammani za ta kasance kan ‘yan adawa idan irin su Gwamna El-Rufai da Gwamna Wike su ka kafa ‘yan sandan kan su a jihohin su?”
Osita ya ce tabbas daga cikin korafe-korafen da gwamnonin su ka yi, akwai abin dubawa. To sai dai bai goyi bayan a kara wa gwamnonin jihohi wasu karfin iko fiye da wanda gare su a yanzu ba. Na yanzu din ma ya yo masu yawa, kuma sun fi kowa take doka.
“Gwamnonin da kuma ke tayar da jijiyoyin wuya kan sake fasalin Najeriya, tunanin su kawai su kara samun kudin shiga. Ka ji tashin-ta-ido. Wai mutanen da su ka hana Majalisar Dokoki ta Jihohi da kotunan jihohin kasar nan cin gashin kai a rika ba su kudaden su kai-tsaye daga tarayya, su ke neman karin kudade kuma.”
Osita ya ce kudaden da ake ba su din ma yanzu ai me za su iya tinkahon sun yi da su don amfana wa jama’ar jihohin su?
Osita ya nemi duk dokar da ta shafi ‘yan Najeriya baki daya, to ta kasance dokar tarayya ce ta kasa gaba daya, don kada wasu tsirarun jihohi su rika kakaba dokar da za ta zamo wa kasar nan jangwangwama daga baya.
Ya na magana ne kan kudirin haramta kiwo sasakai da gwamnonin kudu 17 su ka kakaba a jihohin su.
Discussion about this post