KIDIDDIGAR KASHE-KASHE: An salwantar da rayukan mutum 77, an yi garkuwa da wasu 29 a makon jiya

0

A ci gaba da fayyace kididdigar adadin yawan mutanen da ake kashewa ko sacewa a kowane mako da kowane wata, Cibiyar Nigeria Mourns ta bayyana cewa an kashe mutum 77 kuma aka sace mutum 29 a makon da ya gabata.

Nigeria Mourns ta ce kamar yadda ta saba a al’adance, ta kididdige adadin mutane a rahotannin da jaridu su ka rika bugawa da kuma ta bakin iyalan mamatan ko na wadanda aka yi garkuwa da su din.

Rahoton ya fara da kashe ‘yan sanda uku a Jihar Delta, a waccan Lahadi. Sai kuma kisan da makiyaya su ka yi wa mutum 13 a Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba, duk a ranar Lahadi din.

Akwai kuma wasu mutum 17 da mazaunin garin Bornon Kurku a Karamar Hukumar Bali da su ma aka ce makiyaya su ka kashe.

A jihar Benuwai an kashe mutum hudu, haka aka sace mutane a kullum tun daga Lahadi har zuwa Asabar da ta gabata.

Kuma ‘yan bindiga sun sace alkalin Kotun Musulunci a daidai lokacin da ya ke shari’a, a Bauren Zakata, ciki. karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

A jihar Kaduna ‘yan bindiga sun kashe mufum takwas a Karamar Hukumar Chukun, sai kuma kisan dan Sarkin Kontagona, Bashir Namaska da ‘yan bindiga su ka yi a ranar Alhamis.

A Malumfashin Jihar Katsina kuma an tsinci gawar wani Limamin Coci mai suna Alphonsus Bello, a bayan makarantar horaswa ta Malumfashi.

Nigeia Mourns ta kididdige cewa an bindige mutum 723, an yi garkuwa da mutum 407 cikin watan Afrilu -Rahoto

Kungiyar Nigeria Mourns, mai bin diddigin asarar rayuka a yake-yake da rikice-rikice a cikin Najeriya, ta bayyana cewa a cikin watan Afrilu 2021, akalla an kashe mutum 723, kuma aka sace mutum 407 aka yi garkuwa da su.

Daga cikin wadanda aka kashe din dai 500 duk fararen hula ne, saura 133 kuma jami’an tsaro ne daga bangadorin tsaro daban-daban.

‘Yan bindiga ne su ka kashe mutum 426, yayin da Boko Haram su ka kashe mutum 117. Sauran wadanda su ka rage a adadin lissafin wasu sun mutum a hannun jami’an tsaro, wasu a rikicin ‘yan kungiyar asiri, wasu kuma wurin rikicin kabilanci.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka kashe mutum 1,603, an sace mutum 1,774 a Najeriya.

A cikin rahoton, akalla an samu tabbacin kashe mutum 1,603 a hare-hare daban-daban a fadin kasar nan, tsakanin watan Janairu zuwa Maris, 2021.

Wata kungiya ce mai suna Nigeria Mourns ta tabbatar da wannan kididdigar.

Rahoton na “Munanan Hare-haren Cikin Janairu zuwa Maris 2021”, sun wallafa shi a ranar Lahadi.

Alhamis.

Share.

game da Author