KATSINA: Yadda ‘yan bindiga su ka kwashi masu Sallar Tuhajjud 47 a Masallacin Izala na Jibiya

0

Wasu rikakkun ‘yan bindiga sun kewaye Masallacin Izala na cikin garin Jibiya, su ka yi gaba da masu Sallar Tahajjudi su 47.

Mummunan lamarin ya faru tsakar daren Lahadi, wayewar garin Litinin wajen karfe biyu na dare.

Majiya daga cikin Jibiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa masallatan Izala biyu ne kuma kusa da kusa a Jibiya, a unguwar da ake kira ‘Yan Kwata. Amma dai a masallaci daya su ka kwashi masallatan, ba duka biyu ba.

“Mutum 47 aka yi gaba da su, wadanda su ka hada da mata da kananan yara, amma daga baya mutum bakwai ya dawo.

Lawal Jibiya ya shaida wa Daily Nigerian cewa, “wasu mazauna kauyen Jibiya sun sanar da cewa ga mahara nan sun tunkaro Jibiya. Jin haka sai ‘yan sakai da matasa daruruwa su ka yi gangami su ka tare hanyar da ake tunanin za su shigo garin Jibiya.

“Amma ba mu san yadda aka yi ba, sai su ka canja hanya, su ka shigo ta yamacin gari, maimakon ta hanyar Daddara, Kukar Babangida ko Magama da aka yi tsammani.”

Majiya ta ce sun tunkari masallacin yayin da su ka bulla ta Asibitin Yunusa Dantauri. Kuma ba su yi harbi ko sau daya ba, sai da su ka tattara masallatan su ka yi gaba da su, sannan su ka fara harbe-harben firgita jama’a a sama.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tabbatar da cewa masallacin a bayan gari ya ke, yamma da garin Jibiya.

An Kwashi Mutum 18 Da Rana Tsaka A Garin Tsaskiya:

Rahotanni da wasu kafafen yada labarai a Katsina sun tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa a ranar Asabar ‘yan bindiga sun yi wa garin Tsaskiya tattaki wajen 12 na rana, su ka hargitsa garin da harbe-harben bindiga, kuma su ka kwashi mutum 18, su ka nausa cikin daji da su.

Garin Tsaskiya ya na yammacin garin Dutsinma, amma ya na karkashin Karamar Hukumar Safana.

PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da wani mutumin Dutsinma mai suna Jamilu Ibrahim wanda ya tabbatar da cewa da idon sa ya ga abin tausayi.

“Na ga yadda mutanen garin Tsaskiya ke tururuwa, sun tako kasa zuwa nan cikin garin Dutsinma domin gudun tsira da rayukan su.

“Ina tabbatar maka kuma har yau gwamnatin Jihar Katsina ba yi magana kan mutanen da aka kwasa su 18 a Tsaskiya ba.” Inji shi.

Lokacin rubuta wannan labari dai Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ba ta yi magana ba, amma majiyoyi a Katsina sun ce jami’an tsaro na cewa masallata 11 kawai aka gudu da su a Jibiya.

Share.

game da Author