Karya ne, Shugaba Buhari bai umurci Pantami ya ajiye aiki ba – Binciken DUBAWA

0

Zargi: Wani hoton bidiyon da aka sanya a shafin youtube na zargin cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami ministan sadarwa wato Dr. Isa Pantami

Wani bidiyo a shafin YouTube wanda aka wallafa ranar 20 ga watan Afrilun 2021 na zargin cewa shugaba Buhari ya sallami ministan sadarwa Dr. Isa Pantami.

Dr. Pantami wanda ya sha kakkausar suka dangane da kalaman da ya yi a baya masu nuna kaifin kishin addini ya ja hankalin jama’a sosai a ‘yan kwanakin da suka gabata. Da yawa sun yi kira da ya yi murabus, wasu kuma suka furta akasin haka.

Dangane da wannan bati ne ma ya sa wani bidiyo sa tashar Independent TV7 ta wallafa a shafin YouTube ke zatgin wai shugaba Buhari ya sallami ministan

Mutane 290 suka kalla bidiyon a tsakanin sa’o’i 48 da fitanshi. Mai yiwuwa saboda kanun da aka yi wa bidiyon inda a rubuta Breaking News!! Wato labari da dumi-dumin shi!!! Buhari ya bayar da umurnin sallamar Pantami.

Tantancewa

Na farko dai DUBAWA ta lura cewa bacin wannan zargi, babu wannan labarin ko ina a shafukan yanar gizo, musamman ma a kafofin yada labaran da ke da sahihanci.

Haka nan kuma, shi kan shi labarin na bidiyon ba shi da wani armashi domin a mintocin takwas na bidiyon babu inda aka fito fili aka bayyana sallamar Pantamin karara.

An sa kanun labarin ne kawai dan jan hankalin jama’a domin labarin bai yi bayanin da ya sanya cikin kanun ba.

Lokacin da DUBAWA ta tuntubi malama Uwa Suleiman, wadda ke magana da yawun ministan sadarwar ta wayar tarho, ta karyata wannan zargi. “wannan batun ba gaskiya ba ne ku yi watsi da shi,” ta ce.

Shi kan shi Garba Shehu ya tabbatar cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Ba wannan ne karon farko da DUBAWA ke samun labarai irin wannan ba, wadanda take ko kuma kanun da aka rubuta musu yawanci basu da wata alaka da labarin da ake so a bayar.

Daga Karshe

Bayan cece-kucen da ke kewaye da ministan wato Dr. Isa Pantami, shugaba Buhari bai ce mi shi ya ajiye aikin shi ba. Dan haka zargin karya ce. Taken da aka baiwa bidiyon a shafin youtube ba gaskiya ba ce.

Share.

game da Author