Gwamnatin Jihar Delta ta karyata labari da iƙirarin cewa Gwamnatin Tarayya ta damƙa mata dala miliyan 4.2 na kuɗaɗen satar tsohon gwamnan jihar, James Ibori, waɗanda Birtaniya ta maido wa Najeriya kwaan nan, bayan ta ƙwace su daga hannun James Ibori.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya bayyana wa Kwamitin Binciken Kuɗaɗen Sata cewa an maida kuɗaɗen ga Gwamnatin Jihar Delta.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Ifeanyi Okowa, Olisa Ifeajika, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa har zuwa ranar ko sisin kwabo bai shiga aljihun jihar Delta da sunan kuɗaɗen satar Ibori ba.
Ifeanyi kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES da wasiƙa a ranar, inda ya ƙara jaddada matsayar Gwamnatin Jihar Delta cewa tabbas ba ta kai ga karbar ko sisi ba tukunna.
Sanarwar ta nuna cewa har yanzu Gwamnatin Jihar Delta na tunrubar Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami domin ganin cewa ta karbi kuɗaɗen.
Sanarwar ta kuma shaida wa ɗaukacin al’ummar Jihar Delta cewa Gwamnatin Ifeanyi Okowa za ta yi amfani da kuɗaɗen ta hanyoyin da su ka dace domin samar da ayyukan inganta rayuwa a jihar Delta.
Ta kuma gode wa Gwamnatin Tarayya a ƙoƙarin ta na ganin an maida kuɗaɗen a inda aka sace su, wato jihar Delta.
Sai dai kuma sanarwar ta ce har zuwa Laraba ba a damƙa wa Jihar Delta kuɗaɗen ba.
Discussion about this post