Wasu matasa biyu, Sanusi Ahmed da Rabiu Abubakar sun shiga hannu bayan kama su da jami’an ƴan sandan Kano suka yi suna haurawa gidajen mutane suna yi musu fashin Atamfofi da wasu kaya cikin dare.
Kakakin rundunar Kano, Abdullahi Kiyawa ya bayyana haka a lokacin da yai nuna wadannan matasa wanda dukkansu biyu ƴa shekara 22 ne a hedikwatar ƴan sandan Kano dake Bompai.
Kiyawa ya bayyana cewa bayan kararraki da mazauna unguwar Dawanau suka rika kaiwa ofishin ƴan sanda karin samun yawa-yawan matasa masu fashi suna tsallakawa gidaje suna satan kaya, jami’an suka fantsama farautar su.
Sanusi da Rabiu sunce bayan zannuwa da suke sata a gidanjen mutane wannan karon sun saci batirin Sola a gidan wani da suka afka ma da misalin karfe biyun dare a unguwar Dawanau.
An nunu wadannan barayin rataye da zannuwan da suka sata, bindiga kirar hannu da sharbebiyar adda wanda suke tsorata mutane da su, idan ka ki bada hadin kai kuma su aikata maka.