KADUNA: Gwamnati ta siyo maganin kau da yunwa a jikin yara kanana

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta siyo maganin kawar da yunwa katan 3,450 domin ceto yaran dake fama da yunwa a jihar.

Gwamnati ta kashe Naira miliyan 100 wajen siyo maganin.

Shugaban fannin masana sinadarin inganta garkuwar jiki da abinci na jihar Ramatu Musa ta sanar da haka a hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a garin Kaduna.

Ramatu ta ce gwamnati ta damka maganin ga hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar domin raba wa cibiyoyin kiwon lafiya asibitocin kula da yaran dake fama da yunwa a jihar.

Ta kuma ce gwamnati ta ware naira miliyan 500 domin siyo maganin kawar da yunwa a jikin yara kanana.

“Gwamnati za ta taimaka wajen wayar da kan mutane sanin mahimmancin ciyar da ‘ya’yan su musamman ‘yan kasa da shekaru biyar abinci mai gina jiki da karfafa garkuwar jiki.

Shugaban shirye-shirye na hukumar ceto Yara kanana dake fama da yunwa na jihar Kaduna KADENAP Umar Bambale ya ce kawar da yunwa a jikin yara kanana na daga cikin matsalolin da gwamnati ta sa a gaba domin kawar da matsalolin yunwa da yara ke fama da shi.

Ya ce daga shekarar 2017 zuwa 2020 yara 90,228 ne suka fada matsalar yunwa a jihar inda daga ciki gwamnati ta ceto yara 66,980 daga cikin su.

A watan Maris din 2021 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa yunwa ta darkako Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20 daban-daban na duniya.

Wasu kasashen da hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa yunwa ta nausa kuma ta darkaka sun hada da Afghanistan, Yemen, Congo, Sudan, Habasha, Haiti da Syria.

Wadannan kasashe 20 da hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta lissafa, ta ce nan da ’yan watanni za su iya fadawa cikin halin matsananciyar yunwa, idan ba a gaggauta yin wani kokarin cetar da yankunan ba.

Share.

game da Author