KADUNA-ABUJA: Majalisar Tarayya za ta binciki harkallar siyar da tikitin jirgi kasa da ya kazanta yanzu

0

Majalisar Tarayya za ta binciki harkallar saida tikitin jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja da ya kazanta yanzu.

An maida siyan tikitin jirgin kasan Kaduna-Abuja ta hanyar yanar gizo domin a tsaftace harkar sannan don akau da masu harkallar tikitin suna siyar wa matafiya da dan karan tsada.

Tun a watan Janairu ne hukumar Jiragen Kasa ta Kasa NRC ta maida siyan tikitin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja ta yanar gizo maimakon layi da ake bi a siya a tashar jirgin dake Abuja da Kaduna.

Dan Majalisa Zayyad Ibrahim ne ya ya jagoranci mahawarar a zauren majalisar.

Yace maimakon a samu sauki wahala mutane suka fada ciki tsindum.

” Da farko dai ba a iya siyan tikitin ta yanar gizo, ko shafin ta ki budewa ko kuma ya bude ka iske duk an siye kujerun jirgin.

Zayyad ya ce abin dai ya koma kamar a da, harkalla ma’aikatan suke yi. idan suka siya tikitin sai su rika siyar wa da dan karan tsada a tashar jirgin idan matafiya sun zo.

Abin ya kazanta ta yadda maimakon a samu sauki sai tsananin wuya aka jefa matafiya aka yi.

Idan ba a manta ba makasudin kirkiro siyar da tikitin jirgin ta yanar gizo shine don a dakile harkallar ma’aikatan hukumar da ke nunka kudin tikitin suna saida wa a tashan jirgi wa matafiya.

Majalisar ta amince a gayyato duka jami’an kamfanonin da aka baiwa ikon siyar da tikitin da kuma jami’an hukumar jiragen kasa ta kasa domin su zu su yi bayani a gabanta, sannan su wanke kansu.

Share.

game da Author