Tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Josbua Dogon Yaro ya rasu.
Dogonyaro ya rasu yana da shekaru 80a duniya.
Babban dan sa, Joseph Dogonyaro ya sanar da Kamfanin Dillancin Labarai, rasuwar mahaifin na sa.
” Dama baban mu ya kwana biyu bashi da lafiya, sai dai jikin yayi tsanani ranar Alhamis, da muka ga ya samu shanyewar bangaren jiki irin na farad daya dinnan. Daga nan sai muka dauke shi muka kai shi asibiti.
Har yanzu muna cikin dimuwa da juyayin rashin mahaifin mu.
Ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Jos.