Jihohi ke da hakkin gurfanar da masu laifin satar mutane da hare-haren ‘yan bindiga, ba Gwamnatin Tarayya ba -Lai Mohammed

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jam’iyyar PDP tantagaryar jahila ce, da har ta ke danganta wa Gwamnatin Tarayya kasa gurfanar da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindiga masu kai hare-haren satar dukiyoyi da kisan jama’a.

A ranar Talata ne Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya yi taron manema labarai a Abuja, inda ya tantance cewa, “hakkin jihohin da abin da ya shafa ne su gurfanar tare da hukunta masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan bindiga masu kai hare-haren satar dukiya da kisan jama’a, amma ba hakki ne na Gwamnatin Tarayya ba.

“Laifukan ta’addanci irin na Boko Haram shi ne Gwamnatin Tarayya ke da hakkin gurfanarwa da tabbatar da cewa an hukunta wadanda aka kama.” Inji Lai Mohammed.

Ministan na cike da mamakin da ya ce “jam’iyyar PDP tantagaryar jahila ce, ta shafe shekaru 16 a banza a kan mulki, amma ba ta san bambancin laifukan da su ka shafi tarayya ba daban da na jihohi.

“To laifin garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga laifin da ake yi wa jiha ne. Amma laifin Boko Haram da sauran laifuka na ta’addanci wannan laifin da ake yi wa gwamnatin tarayya ne. Don haka PDP ta daina babatun wai gwamnatin tarayya ta ki gurfanarwa da hukunta masu garkuwa da ‘yan bindiga masu kai hare-hare.” Cewar Lai.

“Saboda jahilci ya yi wa PDP kanta da tsatsa, har jam’iyyar ta manta cewa wannan gwamnatin ta gurfanar da dubban ‘yan Boko Haram a Kainji, kuma yanzu haka gwamnati na samun hadin kai da bangaren shari’, domin ci gaba da shari’ar dandazon ‘yan ta’addar da aka damke a hannu ake tsare da su.” Inji Lai.

Ya ce gwamnatin tarayya ta damu da halin da kasar nan ke ciki, kuma ta na kokarin ganin ta dakile matsalolin baki daya.

Share.

game da Author