Janarori 5 da ke bisa tsanin kaiwa ga maye gurbin marigayi janar Attahiru, COAS

0

Ana sa ran nan ba da dadewa ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai nada sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya.

Sai dai kuma cakwakiyar da ke tattare da wannan nadi dake tafe shine, wa ye Buhari zai nada sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, wato wanda zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim da aya rasu a hadarun jirgin sama a Kaduna.

Jaridar PR Nigeria ta yi nazarin wasu damarai guda biyar wanda sune dai ke bisa layin zama Babban Hafsan Sojojin Najeriya, COAS din.

Duk da dai ana ta watsa cewa wai akwai yiwuwar manjo janar Danjuma Ali Keffi, ne ake kyautata zaton shine zai dare kujerar, masu yun fashin baki a harkar tsaro sun ce idan har hakan zai tabbata sai an yi wa wasu zaratan sojojin Najeriya akalla 30 dake gaba da shi ritaya kafin ya iya zama Babban Hafsan.

Yanzu dai wanda yake kan gaba a zama sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, wato wanda zai maye gurbin Attahiru, shine Manjo Janar Ben Ahanotu, daga Kos na 35, kuma dan asalin jihar Anambra. Shine wanda ya bi Mohammed Yusuf can inda yake boye a farkon Boko Haram ya kamo shi ya danka wa ‘yan sanda.

Sai kuma Manjo Janar MA Aliyu Kos na 36, daga jihar Gombe.

Manjo Janar Yusuf Mano, Kos 37, daga jihar Yobe.

Manjo Janar Farouk Yahaya, Kos na 37, daga jihar Sokoto.

Sai dai kuma duk da wadannan matsayi da suke da shi, shugaban kasa Muhammadu Buhari na da Ikon zabin duk wanda ya ga dama a matsayin sa ba shugaban kasa ko kuma wanda ministan Shari’a ya bashi shawarar ya zaba.

Share.

game da Author