Jam’iyyar APC ta dakatar da Honarabul Gudaji Kazaurae saboda wai yayi wa gwamna Badaru rashin kunya

0

Jami’iyyar APC a jihar Jigawa ta dakatar da fitaccen dan majalisar tarayya da ke wakiltar kananan hukumomin Kazaure, Roni, Yankwashi da Gwiwa a majalisar tarayya, Honarabul Gudaji Kazaure.

Jam’iyyar a mazabar Gudaji ne suka dakatar da shi na wata shida sannan ta kafa kwamitin gudanar da bincike a kai da zai mika rahoton binciken nan da kwana 10.

Jam’iyyar ta zargi Gudaji da furta kalaman da basu dace ba ga gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru bayan kammala zabukan fidda gwanaye na jam’iyyar APC a shirye shiryen zaben kananan hukumomin jihar dake tafe.

Gudaji ya bayyana a shafin Facebook din sa cewa gwamna Badaru yayi watsi da wadanda suka yi mishi gani kashe ni a siyasa, suka bauta masa tun yana jam’iyyar ACN har zuwa yanzu, ya koma ya rungumi makiyar sa a jiki.

” Tambayar da zan yi wa gwamna Badaru shine, ina masoyan sa wadanda suka sadaukar da ran su don shi, suka yi fito-na-fito don shi, suka ka yi gani-kasheni duk don samun nasarar sa, amma makiyar sa ne wadanda ba su kaunar sa ya runguma yanzu.

Gudaji yayi kira ga uwar jam’iyyar a Abuja da shugaba Buhari ya sala baki akan abi da ke faruwa a jihar Jigawa, a ja wa Badaru kunne domin ya saki layi.

Ita ko jam’iyyar APC, a karamar hukumar Kazaure Hassan Lawal ya ce tuni ya rattaba hannu a dakatarwa wanda tun daga mazabar sa ne aka rubuto kuma aka saka hannun dakatar da shi daga jam’iyyar, muma mun jaddada hakan.

Shi ko Jamilu Zaki, shugaban karamar Hukumar Kazaure cewa yayi, Honarabul, Gudaji ya bashi mamaki matuka, domin a cewar sa da shi aka zauna aka tantance yan takarar duka kuma aka amin ce da wadanda suka cancanta su yi takara amma daga baya kuma sai gashi yana fadin abinda ba haka aka yi da shi ba.

Share.

game da Author