Jami’an tsaro sun kama mahaifin da ya rika lalata da ‘ya’yan sa mata uku a jihar Anambra

0

Jami’an tsaro na Sibul Difens, NSCDC, reshen dake jihar Anambra ta kama wani magidanci mai shekaru 48 mai suna Thomas Igbo da aka samu da yin lalata da ya’yansa mata uku.

Igabo ya rika lalata da ‘ya’yan sa wanda suke da shekaru 8, 3 da 1 da rabi.

Shugaban rundunar David Bille ya sanar da haka wa manema labarai ranara makon jiya a garin Awka, jihar Anambra.

Bille ya ce Igabo ya aikata wannan mummunar laifi ne a ranar 25 ga watan Mayu.

“Da muka samu labarin abinda Igabo ya aikata sai muka gaggauta kamo shi.

“Gwajin da likitoci suka yi ya tabbatar cewa Igabo ya yi lalata da yan matan duka su uku.

Mahaifin ‘yan matan ce ya kan kwana da babbar ‘yarsa mai shekara 8 da karfin tsiya, su kuma sauran masu shekara 3 da daya da rabi ya na saka musu yatsu a gaban su ne.

“Na yi lalata da babbar ‘ya ta mai shekara 8 sau daya ne tak shima kuma bawai a hayyaci na nake lokacin ba, na dawo gida ne a buge, shine na tilas ta ta har na aikata hakan.

Bille ya ce za a kai Igabo kotu da zarar a kammala gudanar da bincike akai.

Akarshe yayi kira da yin gargadi ga iyaye su rika maida hankali akan ya’yan su matuka saboda kaucewa aukuwar irin haka.

Share.

game da Author