Majalisar Tarayya ta zargi Minista Malami da hannu dumu-dumu wajen karbar wani kaso daga cikin kudaden da ake kwatowa daga hannun barayin gwamnati da wadanda kasashen waje ke maido wa Najeriya, wadanda barayin gwamnati su ka sata su ka boye a can.
An titsiye Malami ne a ranar Talata, lokacin da ya bayyana gaban Kwamitin Binciken Kudaden Satar da Gwamnatin Tarayya ta Kwato.
Tun a ranar Litinin ce ya kamata Malami ya bayyanaa gaban kwamitin, amma bai bayyana ba sai washegari Talata, jiya kenan.
An gayyace shi ne ya bayyana domin yin bayani, tare da sauran jiga-jigan gwamnatin Buhari da na gwamnatocin da su ka shude, tun daga shekarar 2002 har zuwa na yanzu a 2020.
‘Yan Majalisa Su Ka Haifar Da Kiki-kaka Wajen Aikin Kwato Kudaden Sata -Malami:
Yayin da Minista Malami ya bayyana a gaban kwamiti, bude bakin da zai yi ya fara magana, sai ya fara da dora laifin kiki-kakar da ake samu wajen karbowa ko kwato kudaden sata a kan Majalisar Tarayya.
Malami ya ce tsaikon da aka samu na kin sakin Kudirin Dokar Laifuka ta Musamman (Crimes Bill da Executive Bill), wanda su Malamin su ka tsara aka aika wa Majalisa run cikin 2017, shi ke haifar da hashin hadin kai ko rashin sahihin tsari wajen karbo kudaden.
“Lokacin da mu ka hau mulki, mun taras babu wani shimfidadden tsarin karbo kudaden da barayin gwamnati su ka sace. Sai mu ka aiko da kudirin da za a kafa dokar da za ta tanadi wannan tsari da babu. To ina bakin cikin shaida maku cewa har yau Majalisa ba ta yi komai a kai ba. Da a ce Majalisa ta maida wannan kudiri doka, to da ba mu tsinci kan mu a inda mu ke ciki ba yanzu.” Inji Malami.
Ya kara da cewa su ‘yan majalisa da ke kai a yanzu, ba su yin wani katabus domin taimakawa.
‘Ofishin Ka Na Karbar Kudaden Sata’ -Zargin Shugaban Kwamiti Kan Malami:
Sai da Minista Malami ya yi bayanin sa ya gama, sai ya fara kyarta masa ashana bisa kai. Ya yi ikirarin cewa Ofishin Ministan Shari’a ya na karbar kudaden satar da aka kwato, maimakon ya rika karbar kudsde daga Babban Asusun Kudaden Harajin Gwamnatin Tarayya.
Shugaban Kwamiti Adejoro Adeogun, ya ce Malami na da hannu dumu-dumu wajen kacaccala kudaden satar da ake karbowa daga hannun barayin gwamati.
“Doka cewa ta yi duk wasu kudaden shiga na gwamnatin tarayya, a zuba su cikin Babban Asusun Tara Kudi na Gwamnati, wato ‘Consolidated Revenue Account’.
“Tambayar za na ke maka, shin ofishin ka na Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, ka taba karbar kudade daga Asusun Tara Kudaden Sata wadanda ake kwatowa daga hannun barayin gwamnati?”
Malami: “Ofishi na bai taba karbar ko sisin kobo daga Asusun Tara Kudaden Satar da aka kwato ba, ko sau daya.”
Bayan Malami ya ce bai taba karba ba, sai Shugaban Kwamiti ya daga kwafen takarda, ya nuna masa shaida da hujja cewa:
“Ga shaida da hujja mai nuna cewa a ranar 20 Ga Fabrairu, 2017, Babban Bankin Najeriya CBN, ya kafci kudade ya bai wa ofishin ka.”
Akanta Janar Idris Ya Tsamo Malami Daga Cikin Ruwan Zafi:
Yayin da Malami ke ta dawurwurar bayar da amsar da ta ki gamsar da ‘yan kwamiti, sai Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya tsoma baki, inda ya wanke Malami daga laifin da kwamiti ke ganin ya tafka.
“Ai don an ba ofishin sa kudi daga Asusun Tara Kudaden Sata, ba wani aibi ba ne. Da Asusun Tara Kudaden Sata da Babban Asusun Tara Kudadan Gwamantin Tarayya, duk Danjuma ne da Danjummai.” Inji Idris.
Ya ce dukkan su a karkashin Babban Asusun Bai Daya Na Gwamnatin Tarayya su ke, wato TSA, ko ‘Tresury Single Account’, a Turance.
Discussion about this post