INEC ta damu da yawaitar banka wa ofisoshin ta wuta a jihohin kudu

0

An bayanna cewa banka wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wuta a ofishin ta na Ƙaramar Hukumar Udenu da ke Jihar Inugu, a matsayin wani sabon koma-baya a tsare-tsaren da ta ke yi na shirya zabubbukan da ke tafe nan gaba.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Babban Kwamishinan ta mai kula da Yada Labarai da Wayar da kan Masu Zabe, ya raba a ranar Juma’a.

Okoye ya bayyana damuwa kan yadda yawan kona kayan hukumar a wasu jihohi ta hanyar gobara ya ki ci ya ki cinyewa.

Ya ce, “Yanzu kuma a Jihar Inugu abin ya faru, inda Zaunannen Kwamishinan Zabe na jihar, Mista Emeka Ononamadu, ya kawo rahoton cewa an banka wa ofishin INEC na Karamar Hukumar Udenu wuta.”

Ya ce abin bakin cikin da ya faru din ya auku ne wajen kimanin karfe 8:40 na dare a ranar Alhamis, amma ba a samu salwantar rai ba.

Amma, a cewar Okoye, an yi matukar lalata ginin ofishin, kuma kayan zabe da na aikin ofis duk sun kone duk da kokarin da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu ta yi wajen kashe gobarar.

Ya ce INEC ta ji dadin kokarin da hukumar ‘yan kwana-kwanan ta yi.

Okoye ya ce an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru domin su yi bincike.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na uku da ake sanya wa ofisoshin INEC wuta a kananan hukumomi da ke jihohi uku a cikin kasa da mako biyu.

“Na farko, an lalata ofis din mu na Karamar Hukumar Essien Udim da ke Jihar Akwa Ibom a ranar 2 ga watan Mayu.

“Daga nan sai wutar da ta tashi a ofishin mu da ke Karamar Hukumar Ohafia na Jihar Abiya a ranar 9 ga Mayu.

“Wannan wani ƙarin koma-baya ne ga ayyukan da hukumar ke yi da shirye-shiryen ta na zabubbukan da ke tafe.”

Okoye ya tuno da cewa bayan harin da aka kai a Abiya, hukumar ta yanke shawarar ta kira wani taron gaggawa na kwamitin tuntubar hukumomin tsaro kan zabe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES) a makon gobe domin tattauna wannan abin damuwar wanda ke faruwa.

Ya ce lalata gini da kayan aikin hukumar da ya faru a yanzu a Jihar Inugu ya na bukatar a yi saurin duba matakan da su ka kamata don tsare kayan INEC a dukkan jihohin kasar nan.

“Saboda haka, hukumar za ta kira taron gaggawa na dukkan zaunannun kwamishinonin ta, wato ‘Resident Electoral Commissioners’ (RECs) a ranar Laraba, 19 ga Mayu, a Abuja kafin taron kwamitin na ICCES.”

Sai dai babban kwamishinan ya bayyana kudirin hukumar na ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka ɗora mata, cikin su har da kammala aikin kara yawan rumfunan zabe.

Sauran, a cewar sa, sun hada da ci gaba da rajistar masu zabe (CVR), da ayyukan kara wa ma’aikata karfin aiki, da sake duban fasalin Babban Tsarin Aiki (Strategic Plan) na 2022-2026, da ƙarfafa hulɗa da masu ruwa da tsaki da kuma gudanar da dukkan zabukan da aka tsara za a yi.

A wani labarin mai alaƙa da wannan, an ruwaito Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Inugu, Mista Mohammed Aliyu, ya bada umarnin a binciki gobarar da aka yi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor.

Aliyu ya kuma ce a killace wurin don a samu damar gudanar da bincike don tabbatar da hakikanin abin da ya auku tare da gano irin asarar da aka yi.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, ASP Daniel Ndukwe, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ndukwe ya ce gobarar, wadda ta faru a ofishin INECA da ke Obollo-Afor da ke cikin Yankin Karamar Hukumar Udenu na Jihar Inugu, ta faru ne a ranar 13 ga Mayu, da misalin karfe 9:40 na dare.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta samu kiran koke daga babban ofishin ta na yanki da ke Udenu cewa akwai gobara da ta tashi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor a Karamar Hukumar Udenu.

“Nan take jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin yankin su ka garzaya zuwa wajen, yayin da su ka kira Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu su ka je wurin su ka kashe wutar ba tare da …

Share.

game da Author