Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jindadin su game da rashin halartar shugaban Kasa Muhammadu Buhari jana’izan marigayi Ibrahim Attahiru, babban hafsan sojojin Najeriya.
Marigayi Ibrahim Attahiru ya rasu a hadarin jirgin sama a Kaduna ranar Juma’a.
Duk da cewa shugaba Buhari ya aika da sakon ta’aziyyar sa ga iyalai da yan uwan marigayin, mutane da dama na ganin ba shi da hujjar rashin halartar jana’izar na minti 20 ko 30.
Baya ga wasu tsirarun ministoci da suka halarci jana’izar, hatta gwamnoni Kano suka karkada wajen halartar taron sharholiyar daurin auren dan ministan Shari’a, Abubakar Malami.
” Ni dai ban ji dadin rashin bayyanar shugaba Buhari wajen jana’izar Attahiru ba. Mutuwar farad daya ne fa kuma shine babban hafsan tsaro kasa da bai dade da nada shi ba. Ya dai kama ace shugaba Buhari ya ganganda ya halarci jana’izar.
Ire-iren kalaman da yan Najeriya suka rika yi kenan a shafukan yanar gizo domin nuna rashin jin dadin su kan haka.
” Zama a jirgin sama zuwa faransa shine batu na farko, sannan kuma sai da ya shafe kwanaki a can yana harkokin sa, wato abinda ya kai shi. Amma ace minti talatin da zai ware ya halarci jana’izar ya yi masa wuya. Ni dai ban ga hakan ya da ce ba.