Hukumar Kula da Gidajen Radio da Talbijin ta Kasa (NBC), ta gayyaci Ahmed Isah mai gabatar da shirin Berekete a Gidan Radiyon Human Right da ke Abuja, bisa dalilin gaura wa wata mata mari da ya yi a lokacin da ya ke bagatar da shirin sa.
Mataimakin Daraktan NBC Ekanem Antia ya sanar wa manema labarai a ranar alhamis cewa sun gayyaci Ahmed Isah, saboda hukumar ta damu da abin da ya faru a Human Right Radio.
Antia ya ce gayyatar da su ka yi wa Isah za ta ba hukumar damar ji da sanin takamaimen abin da ya faru har ya kai ga kife wacce ya ke wa tambayoyin da mari, kuma aka nuna kai tsaye a soshiyal midiya.
“Hukumar za ta yi adalci ga dukkan ‘yan kasa da kuma mai gabatar da shirin kuma za a bai wa kowane dan kasa damar tofa albarkacin bakin sa kafin a yanke hukunci.
“Dalili kenan NBC ta aika da takardar gayyata ga Shugaban Gidan Radiyon Human Rights da kuma mai gabatar da shirin, Ahmed Isah su zo su bada bayanin abin da ya fsru.”
Daga nan ya bukaci masu gidajen radiyo su fahimci irin nauyin da ke kan su ganin yadda dimbin jama’a sun maida hankali wajen sauraren su.
Wani shirin Gidan Radiyon BBC ys nuno Ahmed Isah, wanda aka fi sani da Ordinary President ya na dalla wa wata mata mari bisa dalilin ta kona gashin kan wata karamar yarinya.
Tuni dai ya bai wa matar da mara hakuri, ya nemi afuwa ga ‘yan Najeriya da kuma Hukumar NBC.
Discussion about this post