Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

0

Ɗan wasan ƙasar Gabon, Guolor Kanga Kaku ya shiga tsomomuwar zargin kantara ƙaryar shekaru.

Ana zargin Kaku ya rage yawan shekarun da aka haife shi, bayan an gano gaskiyar lamari cewa an haifi ɗan wasan tun kafin 1986, shekarar da mahaifiyar sa ta rasu.

A yanzu dai Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afrika za ta binciki yadda aka haifi Kanga Kaku cikin shekarar 1990, kamar yadda ya ke rubuce a takardun haihuwar sa, amma kuma mahaifiyar sa ta mutu tun cikin 1986.

An sha zargin ‘yan wasan Afrika da dama wajen rage yawan shekarun idan sun fita ƙasashen Turai su riƙa buga wa wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa.

Cikin waɗanda aka zarga a Najeriya, har da Taiye Tayo, wanda akwai ratar bambacin sajen shekaru takwas tsakanin shekarar da ya ce an haife shi, da kuma adadin yawan shekarun tagwan haihuwar sa, domin shi da ɗan’uwan na sa tagwaye ne, waɗanda aka haifa rana ɗaya.

Share.

game da Author