Hotunan jirage masu saukar ungulun marasa lamba da ake zargi suna shawagi a Maiduguri, ba a Najeriya aka dauka ba, daga Amurka ne – BINCIKEN DUBAWA

0

Matsalar rashin tsaro a Najeriya na cigaba da ta’azara sakamakon ayyukan ‘yan tawaye a duk yankunan kasar musamman a yankin arewa maso gabas. To sai dai kuma an dade ana zargin cewa akwai wadanda ke tallafawa wasu daga cikin kungiyoyin irinsu Boko Haram da ma sauran wadanda ke haddasa hare-hare a yankin.

Ranar talata 11 ga watan Mayu 2021 wani mai amfani da shafin twitter da sunan Defense News Nigeria ya wallafa wani labari mai zargin cewa gwamnatin Faransa na tallafawa kungiyoyin tawayen Afirka da kudi. Labarin ya kuma danganta Faransa da karuwar da aka samu a yawan hare-haren kungiyar Boko Haram ‘yan kwanakin nan.

Marubucin, Defense News Nigeria ya bude labarin ne da wasu hotuna uku na jirage masu saukar ungulu marasa lamba wadanda ya ke zargi suna shawagi a dajin Maiduguri suna sauke kaya. Ga bayanin farko:

“Mazauna a kauyuka da dama suna maganan wasu jirage masu saukar ungulu da ke shawagi a dajin Maiduguri suna sauke kaya. Musamman da daddare. Akwai sadda suka ga faduwar daya daga cikin jiragen. Da suka ruga su kai agaji sai suka gamu da wasu turawa biyu suna kona kananan akwatunan da ke dauke da takardan kudi (takardun dalan Amurka dari-dari) kafin suka gudu daga wurin da jirgin ya fadi.”

Labarin wanda ya ce batun ya afku a shekara ta 2015 ya dauki hankali sosai a shafin twitter.

Tantancewa

Dubawa ta tantance hotunan jiragen masu saukar ungulu inda ta gano cewa sun yi mafari ne daga tsoffin rahotanni wasu abubuwan da suka faru a Amurka.

Hoton farko ya yi mafari ne daga wani abun da ya faru a Philadelphia, jihar Pennsylvania. Wani jirgi mai suakar ungulu ne da ya ja hankalin jama’a bayan da ya rika shawagi kasa-kasa kusa da unguwar Mt. Airy da ke Philadelphia daga farkon watan Yuni a shekarar 2017. Daga baya bincike ya nuna cewa kamfanin lantarkin Philadelphia ce ke duba hanyoyin lantarkinta.

Hoto na biyu a labarin kuma, an dauke shi ne daga wani bidiyo a gundumar Medina da ke jihar Ohio, Amurka. Wasu masu mallakar filaye suka dauki hoton bayan da suka ji karar harbin bindiga na fita daga jirgin mai saukar ungulu dake shawagi a saman filayen nasu ranar 15 ga watan Afrilun shekara ta 2016 lokacin da suke farautar aladun daji a wurin.

Dubawa ta kuma gano cewa hoton na uku hoton jirgin FBI ne a yankin Charleston ranar labara 22 ga watan Mayu. A cewar jaridar the post and courier, jirgi mai saukar ungulun ya fita aiki ne sakamakon wata horaswa ta hadin gwiwa tsakanin hukumar FBI da ‘yan sandan gundumar Charleston a jihar South Carolina.

A Karshe

Labarin jirage masu saukar ungulu da ke shawagi a dazukan Maiduguri suna sauke kaya, ya yi amfani da hotuna daga jihohin Pennsylvania, Ohio da South Carolina a Amurka ne a maimakon hotunan da ya kamata su bayyana batun labarin dazukan Maidugurin a zahiri.

Share.

game da Author