HIMMA DAI MATA MANOMA: Na saki harkar tela na kama noma don ciyar da marayu na bakwai – Matar da ke takabar rasuwar mijin ta

0

Josephine Malokwu mai shekaru 51, mace ce mai kokarin sana’a, wadda ta shafe shekaru 25 ta na dinkin tela na kayan mata.

Sai dai kuma ta shiga kaka-ni-ka-yi shekaru biyu da su ka gabata bayan rasuwar mijin ta. Ga zafin rashin miji ga kuma nauyin marayu har ‘ya’ya bakwai da mijin ya mutu ya bari.

A tattaunawar ta da PREMIUM TIMES, ta bayyana yadda ta saki harkar tela ta kama noma da kiwo gadan-gadan don rufa wa kan ta asiri.

“Bayan rasuwar miji na, na fahimci aikin tela ba sana’ar da za ta rike mu ba ce. Ta na bukatar zama wuri daya ka dararrashe ka na ta harba kafafu. Kuma shekaru na sun fara matsawa. Sai na yanke shawarar noma kawai da kuma kiwo.

“Ina kiwon dabbobi kuma ina noman masara da noman rogo. Idan na noma rogon, na kan sarrafa shi zuwa garin rogo.

“Gaskiya ba wasu manyan gonaki na ke nomawa ba. Kauye na koma ina noma gonar da miji na ya bari. Sannan kuma na karbi aron wasu gonakin guda biyu, ina biyan ladar naira 100,000 duk shekara.

“Ina sayar da dabbobin da na ke kiwo ina biyan bukatun gida da kudin. Abinci kuwa idan na noma, duk a gida mu ke ci, saboda mu na da yawa.” Inji Josephine.

Ta ce babbar matsalar ta ita ce rashin jari. Amma idan ta samu jari, to noman ta zai kara bunkasa.

“Gwamnati ko wata hukuma ba ta taba tallafa min ba. Akwai dai ranar da wasu jami’an Ma’aikatar Gona su ka zo su ka karbi suna na da sauran bayanai na. Amma daga bisani na ji labarin wasu sun karkatar da tallafin da aka rubuta za a ba ni.

Josephine ta ce ba ta samun matsala da ‘yan bindiga ko makiyaya a gonar ta.

“Ni gona ta kusa da gari ta ke, makiyaya ko barayin dabbobi ba su zuwa su na yi min sata.” Inji ta.

Share.

game da Author