Har yanzu wadanda suka yi garkuwa da dan majalisan dokokin jihar Nasarawa ba su sako shiba kwanaki biyu da sace shi.
Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da Danbaba da ke wakiltar Nasarawa ta Tsakiya ranar Asabar a hanyarsa ta zuwa Jos jihar Filato daga jihar Nasarawa.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Mohammed Omadefu ya tabbatar da aukuwar haka wa manema labarai a Lafiya
Omadefu ya ce maharan sun sace Danbaba a wani daji dake karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, bayan ya wuce kauyen Andaha dake karamar Akwanga.
Sai dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ba yankin kasar Kaduna bane aka yi garkuwa da dan majalisar.
“Duk na bincika wajen ma’aikatan mu dake aiki a karamar hukumar Sanga kuma sun tabbatar cewa hakan bai faru ba.