Har yanzu babu tabbacin ko an sace wani a hanyar Kaduna-Abuja ranar Juma’a, sai dai jami’an tsaro sun ga wata mota an farfasa ta babu kowa ciki- Aruwan

0

Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaron da suka kai wa matafiya dauki a lokacin da masu garkuwa da mutane suka tare hanyar Kaduna-Abuja a Kurmin Kare basu ce wai an sace wani ba.

Aruwan ya ce ko da aka sanar da jami’an tsaro cewa gashi can fa an tare hanyar Abuja-Kaduna, basu yi wata-wata ba suka kama hanya zuwa wannan wuri.

” Ko da suka isa wurin sun iske dandazon motocin matafiya makil ba su iya wucewa. Jami’an tsaron ne suka bude hanya matafiya suka ci gaba da tafiyar su.

” Jami’an tsaron sun iske motoci biyu babu kowa ciki, daya an farfasa gilasan gaba da baya kuma babu kowa a ciki. Amma ba a san ko maharan sun arce da su bane, domin har zuwa karfe 9:45 na dare ba a san inda suke ba.

” Daga baya an ce wancan da babu mutane ashe boyewa suka yi, sun fito shiga shiga motar su. Ita ko wancan mota kirar Honda har zuwa karfe 9:45 na dare ba a ji wani bayani game da wadanda ke cikin motar ba.

Aruwan ya ce za a ci gaba da sanar da jama’a abinda ake ciki.

Wani matafiya ya bayyana cewa bai taba fadawa cikin tsananin tsahin hankali da fargaba ba kamar yadda ya samu kansa ba a hanyar sa ta dawo Kaduna daga Abuja ba.

” Mu fa muna tafiya ne a mota, kwatsam sai muka afka musu a daidai sun gama tattara wasu matafiya, sun lunkuya da su cikin daji.

” Mu ka tsaya cak da yawan mu matafiya har sai da ‘Yan sanda da sojoji suka iso wurin suka dan yi harbe-harben da zasu yi suka bude hanya kafin muka wuce. Amma ciki na da sauran matafiya sun duri ruwa, gaba daya mun fice daga cimin hayyacin mu.

Sanata Shehu Sani shima ya tabbatar da aukuwar wannan al’ amari, inda ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa ” Yanzu wani matafiyi ya kira ni ya ke shaida min cewa masu garkuwa da mutane sun tare hanyar Abuja a daidai Jere zuwa Katari, suna kwashe mutane. Sun tafi da wasu matafiya.

Wani direba da ke sintirin a hanyar koda yashe ya shaida wa wakilin mu cewa, kuda ya iso wannan wuri sai ya iske motoci suna ta juyawa, wasu kuma sun tsaya cak sun zura wa ikon Allah ido.

Daga baya dai jami’an tsaro ne suka zo suka ta bude hanya kowa ya wuce.

Sai dai kuma a wata sanarwa da kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar da daren Juma’a ya ce ba a samu rahoton an sace wani a wannan hari na ‘yan bindiga ba,

” Jami’ an tsaro basu tabbatar da sace matafiya a wannan hanya ba, sai dai an ga wasu motoci biyu daya an farfasa su daya kuma babu mutane sai kayan su. Daga baya wadanda ke cikin wancan motan sun dawo, na hondan da aka farfasa gilashin shi ne ba a gan su ba har yanzu”.

Idan ba a manta ba, a farkon wannan mako ne mazauna garuruwan dake kusa da wannan titi suka gudanar da zanga-zangar kira ga gwamnati ta kawo musu dauki kan yadda masu garkuwa da mutane suka addabi su a ‘yan kwa akin nan.

Share.

game da Author