Hadarin Jirgin Saman Hafsoshin Sojan Najeriya: Ya Zama Wajibi Ayi Kwakkwaran Bincike Na Gaskiya, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Jiya juma’ah, 21/05/2021, muka samu wani mummunan labari, marar dadi, mai tayar da hankalin ‘yan Najeriya, na hadarin jirgin saman hafsoshin soja a garin Kaduna, wanda yayi sanadiyyar rasuwar babban hafsan sojojin Najeriya, Janaral Ibrahim Attahiru, da dan uwa, Manjo Janaral Abdurrahman Kuliya, da sauran hafsoshin sojan Najeriya, bayin Allah, masu hazaka, masu bautawa kasarsu tsakaninsu da Allah! Ina rokon Allah Ta’ala ya gafarta masu, amin.

To, su dai wadannan bayin Allah sun mutu, kuma ita mutuwa riga ce ta kowa, kuma wani al’amari ne da yake faruwa ga kowane abu mai rai, dukkan mai rai wallahi za ya mutu. Kuma kowace al’ummah ta yarda cewa kowa sai ya mutu. Musulmi da wanda ba Musulmi ba, kowa yasan cewa lallai sai ya bar duniyar nan, ko yaki ko yaso!

Allah Subhanahu wa Ta’ala ya halicce mu, tare da samar da mu a matsayin masu rayuwa a bayan kasa, domin ya jarraba mu. Allah Madaukakin Sarki yace:

“Shine wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku; wane ne daga cikin ku zai fi kyautata aiki.” [Suratul Mulk: 2]

Don haka, duk irin yadda rayuwar mutum tayi tsawo, duk yawan shekarunsa a cikin wannan duniya, duk dadewarsa, duk iya makircinsa, to ko shakka babu, wata rana zai mutu ya koma ga Allah. Kai duniyar nan ma ita kan ta wallahi za ta kare, za ta kuma gushe; dan Adam za’a neme shi ko kasa ko sama a rasa shi, a cikin wannan duniya, zai zama tarihi, ya zamo tamkar ba’a yi shi ba. Abin da kawai zai rage shine, aikin sa, da kuma kirkin da yayi da ayukkansa na alkhairi da ya aikata a lokacin rayuwar sa ta duniya. Rayuwa ta har abada tana gidan lahira. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

“Lallai kuma lahira, tabbas ita ce rayuwa, da sun kasance suna sani.” [Suratul Ankabut: 64]

Annabi Muhammad (SAW), tattare da zamansa mafi soyuwa a wurin Allah, kuma mafi girma da darajar gaba dayan halittar Allah, Allah Ta’ala ya fada masa cewa lallai zai mutu kamar yadda kowane mutum zai mutu.

Sannan shi Manzon Allah (SAW), da gaba dayan halitta, za’a hadu a gaban Allah, a ranar Alkiyamah, domin ayi hisabi a tsakaninsu. Allah Ta’ala yace:

“Lallai ne kai mai mutuwa ne, kuma su ma lallai masu mutuwa ne. Sannan lallai ku, a ranar Alkiyamah, a wurin Ubangijinku, za ku yi ta yin husuma.” [Suratul Zumar: 30-31]

Kuma Allah Madaukakin Sarki ya bamu labarin wasiyar da Annabi Ya’akub (AS) yayi wa ‘ya’yansa cewa:

“Ku sani lallai hakika, Allah ya zabar maku addini, don haka kada ku kuskura ku mutu face kuna Musulmi.” [Suratul Bakara: 132]

Ya ku bayin Allah! Wallahi babu wanda yasan lokacin da ajalin da Allah Madaukakin Sarki ya debo masa zai kare. Babu kuma wanda yasan ko a wane wuri ne Mala’ikan mutuwa zai rutsa da shi. Babu kuma wanda ya isa, ko shi waye, ya canza wannan tsari da shirin da Allah yayi. Allah Madaukakin Sarki yace:

“Kuma ga kowace al’ummah akwai ajali. Sannan idan ajalinsu yazo, ba za’a yi masu jinkiri ba da sa’a guda, ba kuma za su gabace shi ba.” [Suratul A’araf: 34]

Don haka, rayuwar duniya ba komai bace illa wani nau’i na wata gajeruwar tafiya, wadda a karshenta za’a isa gidan lahira.

Ya ku jama’ah! Tun da har Shugaban halitta, Annabi Muhammad (SA) ya dandani zafin mutuwa, to mu sani cewa wallahi kowa ma sai ya dandane ta. Ba wanda zai zauna duniyar nan, ko shi dan gidan waye. Da wanda yayi kisa, ko yasa aka yi kisa, da wanda aka kashe duk mutuwa zasu yi, kuma su hadu a gaban Allah!

Imamul Bukhari ya ruwaito daga Nana Aisha (RA), yadda ta bayar da labarin jinyar da Manzon Allah (SAW) yayi a dakinta, har zuwa rasuwarsa.

Sannan a lokacin da Amru Dan As (RA) yazo rasuwa, an tambayeshi shin yaya yake ji? Sai yace:

“Ji nike yi tamkar sammai sun fado a kai na, kassai kuma sun matse ni.”

Sayyidina Umar Dan Khattab (RA) ya tambayi Ka’abul Ahbar cewa ya siffanta masa yadda mutuwa take. Sai yace:

“Ya kai Sarkin Muminai! Hakika ita mutuwa kamar wani reshe ne mai yawan kayoyi a jikinsa, wanda aka shigar da shi cikin cikin mutum. Bayan kowace kaya ta rike wata jijiya daga jijiyoyin jikinsa, sai kuma a samo wani mutum ma’abucin karfi, ya kama wannan reshen ya fizgo shi da karfi, ya fizgo shi kenan tare da tsoka da jijiyoyin jikin!

Wannan ranar mutuwar fa sai ta riske ni, sai ta riske ka, sai ta riske ki, sai ta riske ku, sai ta riske mu baki dayan mu wallahi, kamar dai yadda ta riski wadanda suka rayu kafin mu.

Wadannan hafsoshin sojojin Najeriya sun rasu, kuma mun yi imani da Allah cewa, lokacin su ne yayi, don haka ba zasu wuce ba. To amma duniya ta shaida, ba zamu boyewa kowa ba, babu munafunci, wallahi muna zargi, kuma zargi mai karfi, cewa kashe su aka yi, domin a binne, ko kuma a boye, ko kuma a dakatar da wasu abubuwa! Don haka, wallahi muna jira, kuma muna sauraro, kuma mun sa ido, ayi bincike, bincike na gaskiya, kuma a sanar da ‘yan kasa sakamakonsa, da kuma sanadiyyar wannan hadarin jirgin saman, domin komai yana da sanadi, da musabbabi!

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, tun farkon hawan ta, tana ware mahaukatan kudade, na fitar hankali, domin sayen makamai a yaki ta’addaci, da magance matsalar tsaro. Kuma ana zargi, kuma zargi mai karfi cewa, an sace kudaden nan, kuma makaman ba’a saye su ba. Domin babu su babu mafarinsu! Irin zargin da ita gwamnatin Buharin tayi wa gwamnatin da ta gabace ta, wato ta Goodluck Ebele Jonathan.

Kuma ana zargin cewa, wannan tuhuma ta sace kudin makamai, a karkashin gwamnatin Buhari, ba’a so aci gaba da shi, shi yasa ake kokarin dakatar da shi ta ko halin kaka, kuma ko da za’a halaka wasu mutane ne!

Sannan da farko, an shedi shi Janaral Ibrahim Attahiru cewa, mutum ne mai gaskiya da rikon amana da tsoron Allah. Shi Mutum ne mai kula da Ibadah sosai, a matsayinsa na Musulmi; kuma a hakikanin gaskiya, an tabbatar da cewa, yana son ya ga bayan ‘yan ta’addan Boko Haram da sauran matsalolin rashin tsaro, da suka addabi kasar nan, domin al’ummar Najeriya su samu zaman lafiya, walwala, da jin dadi. Kuma an yi shaidar shi da cewa mutum ne jarumi, ba ya da tsoro, jarumine na gaske. Dama kamar yadda muka sani, masu son a tabbatar da gaskiya da rikon amana a wannan zamanin, wallahi sun fi kowa shan wahala da fuskantar barazana iri-iri.

Janaral Attahiru yana cikin masu kokarin tona asirin maciya amanar tsaron Najeriya, wadanda suka ci kudin makamai a wannan Gwamnati ta shugaba Muhammadu Buhari, abinda ake ta kokarin ayi rufa-rufa, a bar maganar ta sha ruwa. Shi kuma yaki bayar da hadin kai akan wannan manufa. Hatta ma mai bai wa shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaron Najeriya, ya jaddada abinda Janaral Attahiru ya fada, na cinye kudin makamai da aka yi a wannan Gwamnatin.

Hankalin maciya amanar tsaron Najeriya, da ‘yan koren su ya tashi, sai da suka sa shi kansa mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaron ya fito ya janye maganar sa, kuma ya janye daga goyon bayan Janaral Attahiru akan batun bacewar kudin makamai.

To yanzu don Allah, kuna tsammanin wadannan mutane, zasu bar Janaral Attahiru, mutumin da suke ganin kamar yana so ya kwance masu zani a kasuwa, ya wanye lafiya?

Jama’ah ku sani! Maciya amanar tsaron Najeriya suna cin riba ne fa da matsalar rashin tsaron nan, don haka basu son matsalar ta kare; saboda haka, ta kowace hanya, suna iya zama sanadiyyar rasa rayuwarsa a hadarin jirgin saman da ya faru da shi jiya, a Kaduna, ya mutu, shi da sauran hafsoshin Najeriya da suka rasa rayukan su tare da shi!

Jama’ah, wallahi ina mai tabbatar maku da cewa, akwai wasu mutane a kasar nan da basu son matsalar Boko Haram ta kare, da sauran matsalolin tsaron kasar nan. Saboda sun mayar da ta’addancin babbar haja ko babbar hanyar neman kudi.

Allah ya sani, ta’addancin Boko Haram da sauran matsalolin tsaron kasar nan, wallahi ko ‘yan sandan kasar nan bai fi karfin su ba, balle uwa uba sojojin Najeriya da aka yi shaidar su da jajircewa da kwazo wurin aiki. Amma sai gashi an wayi gari, kamar matsalar tana nema ta gagari duk jami’an tsaron Najeriya, saboda babu gaskiya cikin lamarin, kuma munafunci yayi yawa!

Ya ku ‘yan Najeriya! Wallahi dole ne a fito ayi magana ta gaskiya, koda za’a mutu. Mun yi imani da Allah cewa duk zamu mutu, bamu zo duniya don mu tabbata ba, don haka bai kamata aci gaba da tafiya haka ba a Najeriya, a kyale maciya amanar tsaron kasar nan suyi yadda suka ga dama!

Wallahi kowa zai mutu, sannan duk wanda yake raye a halin yanzu, babu wanda zai kara shekara dari biyu nan gaba a duniya, face duk muna karkashin kasa. Don haka duk mai shirya makirci don a kashe wani, don Allah kar ya fasa, kuma idan ya isa ya tabbata a cikin wannan duniyar, shi kar ya mutu.

Daga karshe, ina roko, Ya Allah, ka karbi shahadar Janaral Attahiru, da Manjo Janaral Abdurrahman Kuliya, da dukkan bayin Allah da suka rasa rayukan su a wannan hadari. Ya Allah ka gafarta masu, Allah ka yafe kura-kuren su, Allah kayi masu sakamako da Jannatul-Firdausi, Allah ka albarkaci zuri’ar da suka bari, amin.

Sannan ina roko, Ya Allah, ka la’anci dukkanin maciya amanar tsaron Najeriya, Allah ka tona asirin su, Allah ka watsa lamarin su, Allah ka kunyata su, amin.

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author