Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ya hori al’ummar jihar su sa ido kuma su kasa kunne sosai, biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa Boko Haram sun bayyana a Bauchi.
Kafin nan, sai da Gwamnatin Jihar Bauchi ta fara yin kururuwar bayyanar Boko Haram sun fantsamo cikin jihar Bauchi, daga makauciyar ta jihar Yobe.
Gwamnatin Bauchi ta ce Boko Haram sun bulla kananan hukumomi hudu, wadanda dukkan su su na makautaka da Jihar Jigawa.
Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi Sabi’u Baba ne a ranar Litinin ya bayyana cewa Boko Haram sun kunno kai cikin Kananan Hukumomin Zaki, Gamawa, Darazo da Dambam.
Ya ce zargin kutsen da Boko Haram su ka yi wa kananan hukumomin ya kara tabbata, biyo bayan wani yunkuri da aka yi na neman lalata drurakun turakun watsa sakonnin sadarwa, wato ‘telecommunication masts’ a Gamawa.
Ganin halin da ake ciki a Jihar Bauchi, sai Gwamna Abubakar Badaru ya gaggauta kiran taro da sarakunan gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da shugabannin hukumomin tsaro a Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa, a Dutse, inda a karshe ya yi kira ga al’umma su gaggauta kai rahoton duk wani ko wata bakuwar fuska da aka gani a yanzu.
Tun da farko sai da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Jigawa, Usman Gwamna ya ce sun samu bayanan sirri da ke nuna ana ganin gilmawar wasu da ake zargin Boko Haram a Gwaram.
Ya ce jami’an sa na bibiyar lamarin.
Idan ba a manta ba, cikin 2020 PREMIUM TIMES HSUSA ta wallafa rahoton musamman kan yadda Boko Haram su ka darkaki Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, bayan sun shafe sama da shekaru goma su na ragargazar Arewa maso Gabas.
Discussion about this post