Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kalubalanci gwamnoni musamman na kudu da ke kira da a sake fasalin kasar nan cewa su farayin gyara ga fasalin jihohin ku kafin ku garzayo Abuja neman a sake fasalin kasa.
” Kai gwamnonin kasar nan basu da kunya, a ce wai kiri-kiri su sun yi babakere sun hana kananan hukumomi, majalisun jihohi da kotunan jihohin su sakat sai yadda suka yi da kudaden su amma suna wage baki a sake fasalin kasa bayan sune suka gurgunta tsarin.
” Akwai fasalin da ya wuce a jihohi ne yanzu. Su fara gyara gida tukunna. An ce a bar kananan hukumomi su ci gashin kan su, ku ce a’a, ku kyale majalisun jihahohin ku su ci gashin kai kun ki, an ce kotuna su ci gashin kai kun ki, har hannu Buhari ya saka amma kun ki, akwai sake fasa ko gyara fasalin kasa da wuce haka ne?
” Idan da za su gyara na su, yau a ce shugaban karamar hukuma na da iko akan kudaden sa, zai iya yin ruwa da tsaki game da harkar tsaro a yankin sa da an samu ci gaba mai ma’ana.
” Majalisun jihohi sun yi shiru ba su iya yin komai a nibohin su sai yadda aka juya su suke tafiya saboda basu da iko akan kudaden su.
Malami ya ce shi kansa gyara ko sake fasalin kasa da ake magana dama ai shine abubuwan da ake so ayi abinda ya kamata a yi dai dai ayi su. Sune gyaran ba rudu ba da cika baki da suke yi.
Discussion about this post