Ministan Kwadago, Chris Ngige ya nada kwamitin mutum 10 su hadu domin tsara yadda za a tunkari matsalar rashin jituwa tsakanin kungiyar Kwadago da gwamnatin Kaduna.
Kwamitin wanda ya kunshi mutun shida daga bangaren gwamnatin Kaduna, hudu daga bangaren kungiyar kwadago.
Kwamitin za su bayyana ranar Talata a ofishin ministan Kwadago.
Gwamnatin Kaduna ta ce ba za ta amince da bukatun NLC ba, abinda ta tsara game da ma’aikatan jihar shi za ta aiwatar.
Sai dai kuma a jawabin da yayi bayan taron, minista Ngige ya ce dole za a bi doka a kowani abu da za ayi musamman wanda ya shafi ma’aikata.
Sannan kuma daga yanzu kada a kuskura a rika muzguna wa mutane idan sun fito zanga-zanga.
A karshe dai ya gargadi bangarorin biyu da su maida wukaken su, su zo a yi sulhu idan ba haka ba kuwa, zai yi amfani da karfin ikon da kokar kasa ta bashi a matsayin minista ya tirsasa duka bangarorin su bi doka dole.
Hakan zai hada har da zuwa kotun bin hakkin ma’aikata idan ya kama dole a yi haka.
Shugabar ma’aikatan jihar Kaduna Bariatu Mohammed ce za ta shugabanci wannan kwamiti na mutum 10.
Shi dai gwamna El-Rufai ya dage cewa ba zai hakura ko ya canja tsarin sa na zaftare ma’aikatan jihar da basu komai a jihar ba.
El-Rufai ya ce in ya kai ga a je kotu ne a shirye yake amma ba zai saduda da bin umarnin kungiyar kwadago ba.
Discussion about this post