Gwamnatin Kaduna na taya iyayen daliban Afaka murnar sako su da ‘Yan bindiga suka yi

0

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na taya iyayen daliban kwalejin Afaka da’ yan bindiga suka saki ranar Laraba.

A sanarwar da Aruwan ya fitar, ya ce gwamna El- Rufai ya hori daliban da su dauki abinda ya faro da su a matsayin wani gwaji a rayuwa.

” ‘Yan sandan jigar Kaduna ta sanarwa gwamnati cewa’ Yan bindiga sun sako daliban kwalejin ayyukan gona da gandun daji 27.

” Gwamnati na taya iyaye da daliban da aka sako murna.

An sako daliban Kwalejin Afaka

‘Yan bindigan da suka sace daliban makarantar koyon aikin gona da gandun daji da ke Afaka, Kaduna sun sake su.

Wani babban Jami’in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun sako daliban.

Daliban makarantar sun shafe kwanaki 55 tsare a hannun yan bindigan bayan gaza biyan su kudin fansa da gwamnatin jiha da na tarayya suka yi.

Maharan sun bukaci a biya su naira miliyan 500 kudin fansa.

Sai dai kuma gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ba za ta biya kudin fansa ga kowani dan bindiga ba.

Hakan ya sa iyayen yaran sun rika yin zanga-zanga domin jawo hankalin gwamnati su tausaya wa yayan su a samu a sake su.

Idan ba a manta ba, an sako dalibai 10 a kwanakin baya, yau kuma an saki sauran 27 da ke tsare a hannun yan bindigan.

Shugaban kungiyar iyayen daliban, Abdullahi Usman ya shaida wa Channels TV cewa an saki daliban da misalin Karfe 4 na yamma.

Share.

game da Author