Gwamnatin Buhari ta yi dalilin sarrafa takin zamani buhu miliyan 30 cikin shekaru hudu – NSIA

0

Shirin Samar da Takin Zamani na Shugaban Kasa ya yi dalilin sarrafa takin zamani mai nauyin kilogiram 50 har buhuna milyan 30 a cikin shekaru uku.

Hukumar NSIA ta Kasa ce ta bayyana haka tare da cewa shirin mai suna Presidential Fertilizer Initiative ya kara yawan masana’antun sarrafa takin zamani daga bakwai zuwa 44.

Haka dai NSIA ta bayyana a cikin rahoton bin-diddigin kudaden ta na 2020 ya tabbatar, wanda aka wallafa a cikin makon da ya gabata.

A ranar 14 Ga Disamba, 2016 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin bunkasa takin zamani, a yayin jawabin kasafin kudi na 2017.

Daga nan shirin ya fara samun gindin zama bayan ziyarar da Sarkin Morocco, Mohammed VI ya kawo ta kwanaki biyu a Abuja, cikin Disamba, 2016. A lokacin ne aka cimma yarjejeniya tsakanin kasashen biyu domin hadin-guiwar samar da takin zamani.

Duk da tinkahon da gwamnati ke yi na samar da takin zamani, manoma da dama na kukan cewa ba su iya samun takin su saya a farashin gwamnati.

Wasu ma na ganin cewa akwai yiwuwar farashin takin zamanin ya karu sosai a daminar bana, fiye da farashin shekarun baya.

“Takin zamani zai wadata a wannan daminar, amma kuma zai yi tsada fiye da tsadar sa ta shekarun baya”. Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Share.

game da Author