Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom ya yi fatali da shirin da gwamnatin tarayya ta ce ta ke yi na ƙoƙarin tsugunar da Fulani makiyaya a wuri ɗaya, domin samar masu rugagen zama su yi kiwo, maimakon karakainar yawon kiwo cikin jeji da su ke yi.
An tsara cewa za a fara shirin cikin wata mai zuwa.
“Wannan shiri bai zo mana cikin mamaki ba, abu ne za a yi wanda kwata-kwata bai dace ba. Wannan fa shi ne ciwo daban, kuma magani daban gwamnatin tarayya ke kokarin yi.
Haka dai Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Ortom, Terver Akase ya bayyana a madadin gwamnan.
Akase ya kara da cewa Gwamnatin Jihar Benuwai ta cika da mamakin cewa, “a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara dugunzuma a ƙasar nan, amma kuma wai gwamnatin tarayya za ta sake buɗe burtaloli ta kafa wa Fulani rugage da dazukan kiwo, saboda ba ta da wani tunanin iya shawo kan matsalar, sai kafa rugage kawai.
“Yanzu dai ta ƙara fitowa fili ƙarara cewa akwai wata boyayyar manufa wacce Fadar Shugaban Kasa ce kaɗai ta sani. Amma idan ba haka ba, duk jihohi ba su goyi bayan kafa wa Fulani makiyaya gandun rugagen kiwo ba, ita kuma gwamnatin tarayya sai ƙumajin kafawa ta ke yi. Saboda haka irin wannan kiwon a wannan zamanin dai tsohon yayi ne. Haramta shi kaɗai shi ne mafita.”
Ortom ya ce ko a cikin watan Fabrairu sai da Gwamnonin Arewa su ka yi taro su ka nuna damuwa kan irin kiwon da makiyayan nan ke yi shi ke haddasa fitintinu da kashe-kashe. Gwamnonin sun ce a yanzu yawan al’umma ya karu sosai. Saboda haka sun amince cewa a fito da tsarin duk makiyayi ya killace shanun sa a garke a wuri ɗaya ya na ba su abinci kasai, shi ne mafita.”
Sannan kuma Ortom ya kara yin tambihi kan yadda gwamnonin jihohin Kudu 17 su ka yi taro a ranar 11 Ga Mayu, su ka haramta gararambar kiwo a jihohin su. Amma kuma duk da haka gwamnatin Buhari na mafarkin kafa gugage da filayen kiwo ga makiyaya.
Haka kuma Ortom ya ce a yanzu a kasar nan babu sauran burtalolin da shanu ke bi su tafi kiwo, saboda duk an gine su, an yi titina, makarantu, asibitoci da filayen jiragen sama da gine-ginen cibiyoyi da hukumomi.
Daga nan sai Ortom ya ce Jihar Benuwai ba za ta bari a kafa mata rugage a bai wa makiyaya filayen kiwo a ciki ba.
Ya ce tuni Bemuwai ta rungumi tsarin kiwon dabbobi a garke ɗaya, ana ciyar da su ba tare da an kwance su sun tafi yawon gararambar kiwo ba, wato ‘ranching.’
Ya ce wanann tsari shi ne hanya mafi sauki ta kawo karshen kashe-kashe tsakanin makiyaya da manoma.