Gwamnatin jihar Kano, asibitin Mamma da gidauniyar Al-Basar sun hada hannu domin yi wa mutum 6,000 masu ciwon ido aiki kyauta a jihar.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Dr Tijjani Hussain ya sanar da haka a taron kaddamar da shirin yi wa mutum 6000 gwaji da aikin ido da aka yi a karamar hukumar Tsanyawa.
Hussain ya ce za a zabo mutanen dake fama da ciwon ido daga kananan hukomi 12 a jihar sannan shirin zai gudana akalla sau biyu a jihar.
Kodinatan hukumar kiwon lafiya a matakin farko na jihar Mr Kamilu Saleh ya ce baya ga gwaji da fidar da za a yi wa mutane Shirin zai bai wa masu fama da ciwon ido magani kyauta a jihar.
Saleh ya ce shirin zai dauki nauyin yi wa mutum 180 masu fama da ciwon ido ‘Cataract’ aiki kyauta sannan a karamar hukumar Tsanyawa kadai za a yi wa mutum 110 dake fama da wannan cuta aiki kyauta.
Dagacen Tsanyawa Alhaji Dayyabu Aliyu ya jinjina wa kokarin da gwamnati ke yi wajen inganta kiwon lafiya a jihar.
Sakamakon wani bincike da aka yi ya nuna cewa ciwon ido wanda aka fi sani da GLAUCOMA ya addabi mutane a kasa Najeriya sannan babban abun tashin hankali shine mutane da dama basu san suna dauke da cutar ba.
Binciken ya kuma nuna cewa cutar na daya daga cikin cututtukan da ke kawo makanta kuma ya fi kama mutanen da suka dara shekaru 40.
Cutar na bayyana ne kamar kwantsa a idon mutum wanda idan ba a yi gaggawar daukar mataki da wuri ba yakan kai ga makanta.
Likitoci sun yi kira ga mutane da su rika zuwa asibiti a kalla sau daya a shekara domin gwajin idanuwarsu.
Yin haka zai taimaka wajen guje wa kamuwa da cututtuka.
Discussion about this post