GAURA MARI: Hukumar NBC ta dakatar da gidan Radiyon ‘Kare ‘Yancin Dan Adam’ mallakin Ahmed Isah daga watsa shirye-shirye

0

Hukumar Kula da Gidajen Radio da Talbijin ta Kasa (NBC) ta dakatar da gidan radiyon Human Right na kwana 30 saboda karya dokar aikin jarida da yayi.

Ahmed Isah, wanda shine mai mallakin gidan radiyo, ya gaura wa wata mata da ta babbake kan wata yarinya yar shekara 8 da wuta a bainar jama’a a lokacin da ake daukan shirin a talbijin.

NBC ta ce bayan wa’adin kwanaki 30 din sun cika, zai kuma biya tara da a ak saka mishi da daukan alkawarin ba zai sake yin irin haka ba.

Idan ba a manta ba Hukumar (NBC), ta gayyaci Ahmed Isah mai gabatar da shirin Berekete a Gidan Radiyon Human Right da ke Abuja, bisa dalilin gaura wa wata mata mari da ya yi a lokacin da ya ke bagatar da shirin sa.

Mataimakin Daraktan NBC Ekanem Antia ya sanar wa manema labarai a ranar alhamis cewa sun gayyaci Ahmed Isah, saboda hukumar ta damu da abin da ya faru a Human Right Radio.

Antia ya ce gayyatar da su ka yi wa Isah za ta ba hukumar damar ji da sanin takamaimen abin da ya faru har ya kai ga kife wacce ya ke wa tambayoyin da mari, kuma aka nuna kai tsaye a soshiyal midiya.

“Hukumar za ta yi adalci ga dukkan ‘yan kasa da kuma mai gabatar da shirin kuma za a bai wa kowane dan kasa damar tofa albarkacin bakin sa kafin a yanke hukunci.

“Dalili kenan NBC ta aika da takardar gayyata ga Shugaban Gidan Radiyon Human Rights da kuma mai gabatar da shirin, Ahmed Isah su zo su bada bayanin abin da ya fsru.”

Daga nan ya bukaci masu gidajen radiyo su fahimci irin nauyin da ke kan su ganin yadda dimbin jama’a sun maida hankali wajen sauraren su.

Wani shirin Gidan Radiyon BBC ya nuno Ahmed Isah, wanda aka fi sani da Ordinary President ya na dalla wa wata mata mari bisa dalilin ta kona gashin kan wata karamar yarinya.

Tuni dai ya bai wa matar da mara hakuri, ya nemi afuwa ga ‘yan Najeriya da kuma Hukumar NBC.

Share.

game da Author