GATARI DA KUDA KOWAR TABA YA SHA KAIFI: Hujjoji 10 Da El-Rufai Ke Garkuwa Da Su Wurin Zabge Yawan Ma’aikatan Jihar Kaduna

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta aiko wa PREMIUM TIMES HAUSA jadawalin adadin kudaden da ta ke karba daga Gwamnatin Tarayya a duk karshen wata, da kuma yadda kusan arankatakaf din kudaden ke tafiya wajen biyan albashin ma’aikatan da ba su ma kai ko mutum 100,000 ba.

Wannan duk wata dabarar sa-toka-sa-katsi da Gwamnatin Jihar Kaduna za a iya yi, ta yi amma babu makawa sai an zabge yawan ma’aikatan jihar.

Ga hujjoji da dalilan da Gwamnatin Jihar Kaduna (GJKD) ta bayar:

1. A cikin watan Afrilu, 2021 Gwamnatin Jihar Kaduna (GJKD) ta bayyana adadin kudaden da ta karba daga Gwamnatin Tarayya da kuma adadin makudan kudaden da ta biya albashi da alawus na ma’aikatan jihar Kaduna, na tsawon watanni shida da su ka gabata zuwa watan Maris, 2021.

Adadin kudaden sun tabbatar da cewa albashin ma’aikatan Jihar Kaduna na lashe kashi 84.97% zuwa kashi 96.63% na kudaden da Gwamnatin Tarayya ke bai wa Jihar Kaduna a duk karshen wata.

2. Cikin watan Nuwamba 2020, Gwamnatin Jihar Kaduna ta karbi naira biliyan 4.83 daga Gwamnatin Tarayya, amma albashin ma’aikata ya lashe naira biliyan 4.66, aka bar gwamnatin Kaduna da balas din naira miliyan 162.9. Kenan mu da ke bukatar ruwa cikin duro, sai ga shi ruwan da ya rage mana ko cikin kofin shan shayi ba su kai ba.

3. Cikin watan Maris 2020, Jihar Kaduna ta tashi da naira miliyan 321 kacal bayan ta biya albashin ma’aikata na naira biliyan 4.498, daga cikin naira biliyan 4.819 da jihar ta karba matsayin kason ta daga Gwamnatin Tarayya na watan Maris.

Wato kenan kashi 93% bisa kashi 100% na kudaden da Jihar Kaduna ta karba, duk sun tafi wajen biyan albashi, babu kudaden da za a yi wa sauran miliyoyin ‘yan jihar Kaduna ayyukan raya kasa kenan.

4. Sauran kudin da su ka rage ba su ma isa a biya kudaden ayyukan yau da kullum, harkar tsaro da sauran kudaden tafiyar da aikin geamnati ba.

Sannan kuma wadancan adadin kudaden da aka kashe, ba a lissafa da albashin ma’aikatan kananan hukumomi ba.

5. Zai yi wahala a tsaya ana wata ja-in-ja da wannan gaskiyar lamarin da ga shi kowa ya gani kuru-kuru babu wata kumbiya-kumbiya.

Sai dai wasu da ba su yarda a rage ma’aikata ba, su na ganin cewa mafi yawan kudaden na tafiya ne wajen biyan masu mukamai na siyasa, ba ma’aikatan gwamnatin jiha ba.

6. To wannan ba gaskiya ba ne. Domin ma’aikatan gwamnatin jiha ne aka biya albashi har na naira biliyan4.498, wato kashi 93.55% bisa 100% na ilahirin kudaden kason da Gwamnatin Jihar Kaduna ta karba a cikin watan Maris 2021, daga hannun Gwamnatin Tarayya.

7. Dududu masu rike da mukamai na siyasa su 337 ne a Jihar Kaduna daga cikin ma’aikatan gwamnatin jihar Kaduna na kai-tsaye, ya zuwa kididdigar watan Maris, 2021.

Wadannan adadin kuwa ba a hada lissafin da ma’aikatan kananan hukumomi 23 ba.

8. An kashe naira biliyan 3.39 aka biya albashin ma’aikata. A cikin su, naira miliyan 259.17 kacal aka kashe wajen biyan albashin masu rike da mukaman siyasa. Sauran naira biliyan 3.13 duk wajen biyan ma’aikatan gwamnatin jiha su ka tafi.

9. Sauran bangarorin da aka biya albashi cikin kudaden sun hada naira miliyan 478 ga ‘yan fansho, sai kason naira miliyan 253.72 da aka biya matsayin gudummawa ga albashin ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko, sai naira miliyan 197.4 na kashi 8% gudummawar asusun fansho da kuma naira miliyan 173.3 da aka biya kudin sallamar masu ritaya.

10. Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta yarda ba, kuma ba za ta amince ta rika daukar kacokan din kudaden da ta ke karba duk karshen wata daga Gwamnatin Tarayya da kudaden da ta ke karba na harajin cikin gida ta rika kashe su arankatakaf a kan ma’aikatan da ko tsirarun mutum 100,000 ba su kai ba.

Saboda haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta maida hankali kan auna muradi da biyan bukatun ma’aikatan jiha a kan mizanin muradu da bukatun daukacin al’ummar Jihar Kaduna.

Wannan shi ne matsayin Gwamnatin Jihar Kaduna (GJKD).

Share.

game da Author