Mazauna garuruwan Garaku, Suleja, Tafa su datse hanyar Kaduna-Abuja, suna zanga zanga-zangar nuna fushin ga mahukuntan Najeriya kan yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wannan yanki.
Daruruwan matasan sun yi dafifi a babban titin bayan sun cinna wa tayoyi wuta, sannan sun hana motoci wucewa.
Wannan hanya dai ita ce hanyar da ta hada kudu da Arewacin Najeriya ta babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Wani da ya yi magana da PREMIUM TIMES HAUSA daga wannan wuri ya bayyana cewa ko a daren Lahadi, mahara sun afka wa garin Garamu, sun waske da mutane shida.
” Sace-sacen mutane ya zama ruwan dare a wannan garuruwa namu. Kullum sai an sace mutane an nemi a biya kudin fansa. Mu dai wannan gwamnati na Buhari ta ishe mu hakannan, gwamnatin tsautsayi kawai.
Wani mai harkar sufiri, Musa, ya bayyana wa wakilin mu cewa, a dalilin haka, matasa sun hana motocin matafiya wuce ta hanyar.
” Yanzu dai ta Jere ake bi, sai a shiga ta cikin Abuja a wuce.
Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis din da ya gabata aka sace mutum 12 a garin Madalla dake kusa da Abuja sannan aka kashe mutum daya.
Tuni dai jami’an tsaro sun isa wannan wuri inda suke ta kokarin tausa matasan su janye daga hanyar.
Yanzu dai da alama ba ‘yan bindiga ba ne kawai ke sana’ ar sace mutane, saboda sakacin gwamnati, an samu labarai masu sahihanci da ke nuna hatta yan iskan gari, makwabta, abokai da yan uwa akan hada baki da su a sace muta a garuruwa.