FATAKEN DARE: Yunkurin barayi na karya kofar gidan Ibrahim Gambari, kusa da Fadar Buhari bai yi nasara ba -Garba Shehu

0

Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa an yi kokarin bankare kofofin gidan Shugaban Ma’aikatakan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari domin a dibga sata, amma ba a yi nasara ba.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya ce an kuma yi kokarin karya kofar gidan Jami’in Ayyukan Gudanarwa na Fadar Shugaban Kasa, Maikano Abdullahi, shi ma ba a yi nasara ba.

Cikin wata sanarwa a shafin Tweeter da Garba Shehu ya fitar, ya ce: “An yi kokarin bankara kofar gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari domin a shiga a yi sata, wajen karfe 3 na asubahin ranar Lahadi, amma ba a yi nasara ba.

“Shi da kan sa Gambari ya tabbatar da cewa wasu wawaye sun yi kokarin shiga gidan sa, amma ba su yi nasara ba.”

Titi ne ya raba gidan Ibrahim Gambari da Fadar Shugaban Kasa.

Haka kuma gidan Maikano Abdullahi shi ma a kan titi daya su ke da na Gambari.

“Haka nan kuma ‘yan sanda na farautar wanda ya yi kokarin karya kofar gidan Jami’in Ayyukan Gudanarwa, Maikano Abdullahi domin ya shiga ya yi sata, amma bai yi nasara ba.”

Sai dai kuma jaridar ‘Online’ mai suna Peoples Gazette, ta buga labarin cewa an shiga a ranar Lahadi barayi sun shiga gidajen sun dibga satar kudade da dukiya. Amma dai PREMIUM TIMES HAUSA ba ta tabbatar da ikirarin wannan jarida ba.

Share.

game da Author