ELRUFA’I, KADUNA DA NLC: Manuniya ga matasan mu, Daga Ahmed Ilallah

0

Ba abune mai iyuwa ba gwamnati taba kowa aikin albashi, amma aikin gwamnati shine samar da yanayi ma kyau da zai bawa al’umma damar samun aikin yi, da samar da abubuwan raya kasa da zai bunkasa tattalin arzki, da al’ummah zasu sami aikin yi, su tallafa wajen raya kasa.

Babban kalubalen da ke damun jahohi da kananan hukumomi a yau shine karancin kudi, ta yadda kudaden da suke samu yana karewa ne akan aiyukan yau da kullum na tafikar da gwamnati, wanda biyan albashi ke kan gaba.

Duk da kasancewar cigaban zamani ya nunan manuniyar cewa, hukumomin gwamnati basa bukatar yawan maaikata don gudanar da aikin gwamnati, musamman bisa cigaban da fasahar sadarwa ta zamani ta kawo (ICT), aiyuka da yawa sun kau, na’urorin computer da smartohones, sun kwace aiyukan mutane da yawam ba kawai a nijeriya ba ama duniya baki daya, misali kamar yadda jaridar Forbes ta bayyanam 20% na mutanen USA suna aiki ne a gona, amma yanzu 2% suke samar da duk abinicin da USA ke bukata har ma su fidda kassashen waje.

Cigaban da ICT ta kawo, wanda ya zamanto kalubale akan ma’aikata sun hada da chanja tsaretsren aiyuka, mussamman na akawu (account), a yau ba a bukatar duk wata a tsara jadawalin albashi, saboda an shigar da shi a computer, ana iya aiwtar da shi cinkin kankanin lokaci ga kuma karancin kuskure da almundahana, haka zalika tsarin fansho da sauransu. Wannan ya sanya ba a bukatar yawan ma’aikatan account, bangarori da dama na aikin hukuma ya samu wannan kalubalen. A yau hattata aikin lafiya da aikin gona cigaban zamani ya sanya ba a bukatar ma’aikata masu yawa.

Annobar CORONA (Covid 19), ya kamata ya zame mana darasi cewa. mutane kalilan kan iya tafiyar da aikin gwamnati, domin ma’aikata mafi yawa sun share kusa da shekara, basu ne aiki, a ma’aikatun gwamnatin tarayya da ma jahohi, musamman tsaka-tsaka da kananan ma’aikata, har yanzu a wasu jahohin ance suyi aiki a gida, Duk da haka chanjin da aka samu kalilan ne.

Duk da wannan kaluabalen, munufar fasaha zamani itace samawa miliyoyin al’umma aikin, ba sai sun dogara da gwamnati ba, ICT ta kawo cigaban rarraba aiyukan da banki da ya keyi shi kadai, ga dubban al’ummah ta hanyar POS centrs, quick teller momo agent da sauransu. Wannan ba karamar dama bace t dogaro da kai ga matasanmu maimakon sanya ido ga aikin gwamnati.
Matakin da jahar Kaduna ta dauka, mataki ne mai tsauri da daure kai, amma fa tunannin jahar kaduna na tattala kudaden al’ummah da gyara fasalin kannan hukumomi, bai sabawa na sauran jahohi ba, musamman ma na arewa.

A yau jahohi da yawa basa iya daukan ma’aikata duk da ana ritaya, wasu basa iya biyan fansho, wasu da kyar suke iya biyan albashi. Ya kamata mahukunta da al’ummominmu suyi hangen nesa kuma ayi karatun ta nutsu.

Hukumomin gwamnati da yawa sun jima da daukan mataki na rage aikin dindin din (permanent & pensionable) ta hanyar bada kwangilolin wasu aikukan, kamar cleaning, securitym har ma da wasu aiyuka na akawu, duk a mataki na dabara don rage nauyi ga hukumomin. ya kamata a lura a kuma yi hangen nesa a kan matasan mu.

Tabbas, akwai babban kalubale akan matasan mu, lokaci fa ya yi da za’a rinka karatun yin sana’a, amma ba karatu da tunanin samun aikin gwamnati ba, don guraben aiki a gwamnati kalilan ne, kuma kullun tsukewa yake, ya zama dole a zama ana hangen nesa.

Jahohin kudu maso yamma kashi 20% kachal ne na masu aikin yi, gwamnati ta basu aiki, 80% masu zaman kansu ne, duk da su suke bada sama da 60% na harajin da Nijeriya take samu.

Mahukuntan gwamnati ya kamata su samar wa al’umma yanayi mai kyau da samar da aiyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki.

alhajilallah@gmail.com

Share.

game da Author