EFCC ta damki wuyan Ahmed tsohon gwamnan Kwara, ta na neman naira biliyan 9 cikin aljifan sa

0

Hukumar EFCC ta gayyaci Tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ta na neman ya yi bayanin yadda naira biliyan 9 su ka salwanta a lokacin mulkin sa.

An gayyaci Ahmed zuwa Hedikwatar EFCC da ke Jabi Abuja, inda ya isa bayan karfe 10 na safiya.

Majiya daga cikin EFCC ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa har zuwa karfe 7 na dare, tsohon gwamnan wanda ya yi mulki tsakanin 2011 zuwa 2019 a karkashin jam’iyyar PDP na tsare a ofishin hukumar.

An ce har dare ya na ta shan ruwan tambayoyi tare da rubuce-rubucen ba’asin abubuwan da ya sani dangane da zargin salwantar wasu kudade.

Ahmed wanda na hannun daman tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ne, ya yi kwamishinan harkokin kudade a Jihar Kwara a lokacin da Saraki ya ke gwamnan jihar.

Ko a baya sai da aka tsare tsohon kwamishinan kudi na jihar Kwara a zamanin mulkin Ahmed, bisa zargin bacewar naira milyan 418 a lokacin mulkin su.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujeran ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an gayyaci tsohon gwamnan na Kwara zuwa ofishin EFCC.

Sai dai har yanzu PREMIUM TIMES ba ta sani ba shin a gida Ahmed ya kwana, ko a gadurum a ofishin EFCC.

Share.

game da Author