EFCC: Bawa da sauran jami’an hukumar sun yi rantsuwar kaffarar fallasa bayanan sirrin gwamnati

0

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da sauran jami’an hukumar, sun yi Rantsuwar Haramta Fallasa Sirrin Gwamnatin Tarayya.

Kakakin Yada Labarai na EFCC Wilson Uwujeran ya bayyana cewa wannan rantsuwa ta na da muhimmanci matuka, domin za ta kara taimakawa wajen daina fallasa sirrikan bayanan gwamnati da ba a son jama’a su sani.

Ya kara da cewa za kuma ta kara karfafa ayyukan EFCC sosai. Uwujeran ya ce Shugaban EFCC, Bawa da kan sa ne ya fara yin rantsuwar, daga nan sauran jami’ai su ka biyo baya.

Yadda Dokar Rantsuwar Ta Ke:

Dokar Haramta Tonawa ko Fallasa Sirrin Gwamnatin Tarayya ta 1962, ‘Official Secret Act’ 1962, ta haramta wa kowane ma’aikacin gwamnati fallasa duk wasu bayanai na sirri na gwamnati, ga wani wanda duk ba a yarda ya bayyana bayanan a madadin gwamnati ba.

“Dokar ta haramta wa duk wani da gwamnati ba ta yarda ya sani ko ya mallaki bayanan ko ya watsa su ba, matsawar dai ba shi ne gwamnatin ta amince ya mallake su ba.

“Duk jami’in gwamnatin da ya karya wannan dokar, ya yi laifi.”

Hukuncin Karya Dokar Fallasa Bayanan Gwamnatin Tarayya:

Sashe Na 7 dokar ya tanaji daurin shekaru 14, ko shekaru 2 da tarar naira 200 ko duk gaba dayan. Ko kuma daurin watanni 3 da tarar naira 100. Ya danganci girman laifin da mutum ya aikata ko girman sirrin da ya fallasa.

Share.

game da Author