Kammalawa: Wannan shi ne ƙarashen rubutun da aka buga ranar Lahadi da ta gabata.
Masu karatu zai yi kyau a wannan makon na waiwaya baya, domin a fahimci asalin Falasɗinu ɗin kan ta, sai kuma asalin Jerusalem, babban birnin Yahudawan Isra’ila.
Tarihi ya nuna cewa Annabi Ibrahim (AS) ya isa yankin Falasɗinu shekaru 3000 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Wato 3000 BC. Ya isa yankin daga Ur cikin ƙasar Iraƙi.
Zaman sa a yankin Falasɗinun wancan zamanin ne ya haifi Annabi Ishaƙa (AS), mahaifin Annabi Dauda (AS). Shi kuma Annabi Dauda (AS), shi ne ake kira Isra’ila, kuma shi ake wa Yahudawa laƙabin ‘Ya’yan Isra’ila, wato ‘Bani Isra’ila’.
Falasɗinu ta samo asali ne lokacin da ƙabilun Keretaniyawa da su ka mamaye yankin su ka cuɗanya da Kan’anawa, su kuma Kan’anawa da ya ke su ne mafi rinjaye, sai su ka narku da Larabawa.
Annabi Dauda (AS) Daular Jerusalem, ta zama matattarar Yahudawa, saboda yawan hare-haren da ake kai masu a lokacin.
Daga shekaru 1000 kafin haihuwar Annabi Isa a Nazareth har zuwa shekaru 580 kafin haihuwar sa, Jerusalem da sauran garuruwa sun sha fama da yaƙe-yaƙe da hare-haren da tilas Yahudawa su ka tarwatse, akasarin su su ka koma cikin Falasɗinawa.
A ƙarƙashin mulkin mallakar Romawa ne aka haifi Annabi Isa (AS) a yankin.
Falaɗinawa Da Isra’ilawa Bayan Nasarar Salahuddeen Ayyubiy Kan Kiristocin ‘Crusade’:
Bayan nasarar Nuruddeen Zangi da Salahuddeen Ayyubiy a yankunan Falasɗinu da sauran ƙasashe irin su Masar, an shafe shekaru ɗaruruwa ana rikice-rikice a yankunan jifa-jafa.
Haka kuma yankin ya kasance ƙarƙashin dauloli daban-daban, har zuwa 1917, shekarar da yankin Falasɗinu ya kasance a ƙarƙashin mulkin Turawan Birtaniya, daga 1917, zuwa 1948, shekarar da Majalisar Dinƙin Duniya (UN) ta ƙirƙiri ƙasar Isa’ila, bayan Yaƙin Duniya Na Biyu.
Yaƙe-yaƙe Tsakanin Isra’ila Da Kasashen Larabawa Daga 1948 Zuwa 2006:
Cikin 1947, bayan gama Yaƙin Duniya na Biyu ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartas da Ƙudiri na 181, wato Kudirin Kafa Ƙasar Isra’ila cikin yankin Falasɗinu.
An raba Falasɗinu wadda ke ƙarƙashin mallakar Turawan Ingila zuwa gida biyu, inda bangare ɗaya ya zama ƙasar Isra’ila, cikin 1947.
A cikin 1948 zuwa 1949, an gwabja yaƙi tsakanin Isra’ila da Falasɗinu, kuma daga nan ne sauran ƙasashen Larabawan yankin su ka fara ƙazamar zaman maƙautaka da Isra’ila.
Cikin 1956 an gwabza ƙazamin yaƙi tsakanin Isra’ila da Masar. A shekarar ce Masar, a ƙarƙashin mulkin Gamel Abdulnaseer ta sa dakarun ta su ka datse Mashigar Tekun nan ta Suez Canal, ta yadda jiragen ruwan Isra’ila ba za su iya ƙarasawa ƙasashen Birtaniya da Fransa. Haka su ma na Birtaniya da na Faransa ba za su iya isa Isra’ila ba.
Kuntunguila Da Algungumancin Birtaniya Da Faransa:
Ganin abin da Masar ta yi wa Isra’ila, sai Birtaniya da Faransa su ka zuga Isra’ila cewa ta afka wa Masar da yaƙi gadan-gadan. Idan ta mamaye wasu yankuna, sai su Birtaniya ɗin da Faransa su shigo matsayin ‘yan sasantawa. Daga nan sai sojojin Birtaniya su ƙwace ikon ruwa da Mashigin Suez Canal daga hannun sojojin Masar. Kuma hakan aka yi.
Cikin 1967 an gwabza ƙazamin yaƙin kwanaki shiga tsakanin Isra’ila da Masar, Jordan, Lebanon da siriya.
Sai kuma yaƙin cikin 1973, wanda a Ranar Bikin Sallar Yahudawa, ƙasar Masar ta danna ɗimbin dakarun ta cikin Isra’ila, ta Mashigar Suez Canal. Su kuma dakarun Syria su ka danna cikin Isra’ila ta Tuddan Golan.
Isra’ila ta sha kashi sosai, duk da dai ita ma ta danna sojojin ƙasashen biyu baya.
A ƙarshe dai cikin 1974, an ƙulla yarjeniyoyin janyewar sojojin ƙasashen biyu cikin Isra’ila.
Yarjejeniyar Camp David (Camp David Accord):
Ranar 26 Ga Mayu, 1979 ce aka ƙulla yarjejeniya tsakanin Masar da Isra’ila domin kawo ƙarshen yaƙin da su ka shekara 30 su na gwabzawa a tsakanin su.
Cikin 1982 Isa’ila ta mamaye wasu yankuna na Lebanon, saboda aushin yadda ƙasar ke goyon bayan Kungiyar Nema wa Falasɗinawa ‘Yanci, PLO. An yi ta kai ruwa rana har sai cikin 1985 sannan dakarun Isra’ila su ka kammala janyewa daga Lebanon, bayan ƙasar ta amince ta kori ‘yan PLO daga Beirut.
An sake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Lebanon cikin 2006, biyo bayan haushin goyon bayan da Lebanon ke bai wa ‘yan ƙungiyar Hizbullah, masu kai wa Isra’ila hari.
Tsakanin Isra’ila Da Fakasɗinu A Yau:
Kusan in banda Lebanon, sauran ƙasashen Larabawa sun zuba ido sun ƙyale Isra’ila na ci gaba da mamaye yankin Falasɗinu. Tuni ma wasu ƙasashen sun maida ko sun koma su na yin hulɗar jakadanci da Isra’ila. Su kuma al’ummar Falasɗinu, an bar su babu ƙarfin sojoji, babu na tattalin arziki. Sai dai ƙarfin hali, wato intifada, faɗa da mai ƙarfin da ba zai taba barin ka samu ‘yancin ka ba. Saboda tsoron kada ‘yancin ka ya sa ka yi ƙarfi da yawan da za ka fi ƙarfin sa.