Bisa dukkan alamu dai hare-haren banka wa ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa, INEC wuta da ake yi a wasu jihohin kudancin kasar nan, bai kawo tawaya ga aikin tsara rajistar masu zabe ke yi ba.
Ko a karshen makon da ya gabata an banka wa Hedikwatar INEC ta Jihar Inugu wuta.
Harin banka wutar na baya-bayan nan dai shi ne na hudu a cikin makonni hudu a kudancin kasar nan.
Amma kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta na nan kan bakan ta na yin aiki da jadawalin da ta tsara na ci gaba da aikin rajistar masu zabe daga ranar 28 ga Yuni a duk faɗin kasar nan.
Mista Festus Okoye, wanda shi ne Babban Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zabe da yada labarai, shi ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi.
Okoye ya ce hukumar na nan kan bakan ta, musamman da yake ta samu gidan yana wanda za a yi amfani da shi a wajen aikin.
Ya ce, “An kusa kammala gina gidan yanar yin rajista ta hanyar intanet kuma za a yi aiki da shi wajen yin rajistar masu zabe wanda za a fara a ranar 28 ga Yuni.
“An gwada gidan yanar an yi ‘yan gyare-gyare. Zai kasance ya na da maganadisun da ke nuna yankunan da ake yin rajista da kuma rumfunan zabe.
“Hukumar na ci gaba da aikin ta kuma ta na aiki a cikin tsarin da ta yi na lokuta.”
INEC ta riga ta tsaida 28 ga Yuni a matsayin ranar da za ta ci gaba da aikin rajistar masu zabe wanda ta dage a baya, kuma ta shigo da sabuwar hanyar kimiyya.
Kwamishinan ya kuma lissafa wasu muhimman ayyuka wadanda za a yi a cikin lokutan da aka tsara, kafin a kai ga ci gaba da aikin rajistar.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya riga ya bayyana cewa za a ci gaba da aikin har zuwa kashi na uku na shekarar 2022.
Haka kuma Yakubu ya bayyana cewa hukumar za ta maye gurbin tsofaffin na’urorin daukar bayanai kai-tsaye, wato ‘direct data capture (DDC) machine,’ wadanda aka shigo da su a cikin 2011, don yin rajistar masu zabe, da sabuwar hanyar fasaha mai suna ‘INEC Voter Enrolment Device’ (IVED).
A cewar sa, wadannan sun hada da faɗaɗa hanyoyin da masu zabe za su samu rumfunan zabe ya zuwa ranar 11 ga Mayu, da gina tare da gwada gidan yanar yin rajista ya zuwa ranar 15 ga Mayu da kuma isowar sababbin na’urorin IVED ya zuwa ranar 31 ga Mayu.
Ya lissafa wasu ayyukan da su ka hada da daukar ma’aikatan rajistar aiki tare da horar da su, ya zuwa 14 ga Yuni, da kuma ci gaba da aikin rajistar a ranar 28 ga Yuni.