Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, ya bayyana cewa Buhari ya wuce-makaɗi-da-rawa wajen busar-iskar da ya yi ya saka hannu kan Dokar Shugaban Ƙasa ta 10.
Wannan doka dai ita ce ta tabbatar wa kotunan jihohi da Majalisun Dokokin Jihohi ‘yancin cin gashin kan su.
Wanann ‘yanci ya na nufin Gwamnatin Tarayya za ta daina tura kuɗaɗen da ta ke bai wa Majalisun Dokoki da Kotunan Jihohi ta hannun gwamnonin jihohi.
Wato za su riƙa karbar kuɗaɗen su kai-tsaye daga gwamnatin tarayya.
Tsaiko, bata lokaci da ƙin fara ba su wannan cin gashin kai ne ya kai ga Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Najeriya (JUSUN) ta tafi yajin aikin da kotunan ƙasar nan manya da ƙanana su ka shace watanni biyu a kulle.
Gwamna Tambuwal, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya ce Shugaba Buhari ya ɗibga kwakyariya, saboda bai tsaya ya tuntubi wadanda ya kamata ya tuntuba ba, sai kawai ya maka hannu a kan dokar. Haka Tambuwal ya bayyana a ranar Laraba, a garin Ado-Ekiti.
Ya yi wannan kakkausan bayani kan Buhari ne a taron tara Antoni Janar Ayodeji Daramola na Jihar Ekiti yin ritaya daga aiki lami lafiya.
Tambuwal ya ce wannan doka ta kai zama haramtacciya, domin Shugaba Buhari shi kaɗai ya yi kiɗan sa ya yi rawar sa, bai yi shawara da wadanda ya kamata ya fara tuntuba ba tukunna.
Tambuwal, wanda ba ya ga cewa lauya ne, ya taba riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Tarayya, kuma ɗan jam’iyyar PDP ne, ya ƙara da cewa gwamnonin Najeriya 36 ba su ƙi goyon bayan ‘yancin kotunan jihohi da majalisun dokokin jihohi ba.
Ya ce kawai dai wasu da ba su san illar abin ba su ka shawarci Buhari ya sa wa dokar hannu, wadda doka ce da za ta zama kamar maƙarƙashiyar karya fukafikin ƙarfin ikon gwamnoni.
Tambuwal ya ƙara da cewa amma dai yanzu an cimma matsaya, gwamnoni sun amince.
Sai dai kuma ya kara da cewa, “mun nuna tirjiya ne, saboda a matsayin mu na gwamnonin Najeriya, akwai nauyi a kan mu wajen fitowa mu nuna wa Shugaban Ƙasa inda ya yi wani babban kuskure, musamman kuma a kan batu da ya shafi dokar ƙasa.”
Discussion about this post