Mambibin Majalisar Tarayya sun soki yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wa zargin da ake wa Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwa (NPA), Hadiza Bala rikon-sakainar-kashi.
Dalilin Haka ne a ta bakin Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi Elumelu, su ka nemi Hukumar EFCC ta binciki zargin da ake yi wa Hadiza kai-tsaye.
“Ai shirme ne a ce wai an kafa mata kwamitin binciken cikin gida, bayan shi Minista Amaechi da kan sa ya aika wa Shugaban Kasa rahoton kin zuba naira biliyan 165 cikin asusun Gwamnatin Tarayya. Saboda haka wannan binciken aikin EFCC ne, bai aikin kwamitin cikin gida ba.
“Kuma fitowar da Minista Amaechi ya yi ya ce Hadiza ta ki zuba naira biliyan 165 a asusun gwamnati, ya nuna irin kamshin turaren sata kala daban-daban da gwamnatin-APC ke fesa wa jikin ta.”
Elumelu ya ce abin da kawai ya rage, tunda an dankara wa Hadiza Bala wannan zargi, abu mafi dacewa kawai EFCC ta fara binciken-kwakwaf, idan an same ta da laifi, sai a gurfanar da ita kotu kawai.
“Amma kafa wani kwamitin bincike na cikin gida, wani yunkuri ne na binne kakudubar da aka tabka tare da wasu manyan jiga-jigan cikin gwamnatin APC.
Ita ma jam’iyyar PDP cewa ta EFCC ce ya kamata ta binciki Hadiza Bala, ba kwamitin bincike ba.