Dalilin dakatar da Hadiza Bala, ‘yar-lelen El-Rufai daga Shugabancin NPA-Fadar Shugaban Kasa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala-Usman.

Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar cikin dare a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an dakatar da Hadiza domin ta kauce a samu damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ogan ta, Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ke yi mata.

Yayin da sanarwar ba ta fayyace irin zarge-zargen ba, Shehu ya ce Buhari ya amince da nada Mohammed Koko a matsayin Manajan Daraktan Hukumar NPA na riko kafin a kammala bincike.

Kafin nadin da aka yi masa na shugabancin riko, Koko shi ne Babban Daraktan Harkokin Kudade na NPA.

Bayan amincewar da Buhari ya yi kan shawarar Amaechi ta a kafa kwamitin bincike, ya kuma amince da nada Daraktan Harkokin Sufurin Jiragen Ruwa na Ma’aikatar Sufuri ta Kasa, a matsayin Shugaban Kwamiti.

Sai kuma Mataimakin Daraktan Harkokin Shari’a na Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta Kasa a matsayin Sakataren Kwamitin Bincike.

Sauran mambobin kwamitin dai Amaechi ne zai bayyana sunayen su.

Hadiza Bala-Usman ta yi suna wajen shiga gaban raji da karajin zanga-zangar #BringBackOurGirls, a lokacin da Boko Haram su ka kama daliban sakandaren mata ta Chibok, a zamanin mulkin Jonathan.

Da ita aka rika yin zaman-dirshan da masu yi wa gwamnati zanga-zanga su ka rika yi a Dandalin Unity Fountain da ke kusa da otal din Hilton a Abuja.

An daina jin karaji da kururuwar ta idan an saci dalibai tun bayan nada ya shugabancin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa cikin 2016.

Bayan wa’adin shugabancin ta ys cika, Buhari ya sake kara mata wasu shekaru hudu a cikin watan Janairu, 2021din da ya gabata.

Hadiza ta yi jajirtacciyar siyasar adawa da mulkin Goodluck Jonathan tun a karkashin rusasshiyar jam’iyyar CPC, har zuwa karakainar kokarin yin ‘maja’ da jam’iyyar AD ta su Bola Tinubu, wadda daga nan aka kafa APC.

Share.

game da Author