Dalilin da ya sa na canja sheka daga PDP zuwa APC – Gwamna Ayade

0

Gwamnan jihar Cross Rivers ya bayyana wasu kwararan dalilin da ya sa ya canja sheka daga PDP zuwa APC.

Farfesa kuma gwamnan jihar Cross Rivers Ayade ya canja sheka a fadar gwamnati dake Cross Rivers ranar Alhamis.

Shugaban Jam’iyyar APC kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya sanar da wannan babbar kamu da APC ta yi a taron jigajigan ‘yan jam’iyar a jihar.

” Abinda Buhari yake yi a kasar nan sune suka birgeni, suka sa na yi shawa’awar shiga APC har ya kai ni ga shiga yau APC. Buhari na bukatan hadin kai daga duka gwamnonin kasar nan domin a samu ci gaba mai ma’ ana. Hakan ya sa na tattara kaya na na koma jam’iyyar APC.

” Ni a ganina ba jam’iyya ba ce yaka mata mu rika dubawa, ya kamata mu sa kasa ce a gaba. Idan muka yi haka to zamu samu nasaravwajen kau da duka matsalolin da suka addabe mu a kasar nan.

” Don haka ina kira ga sauran gwamnoni su zo a hada kai a yi abun da ya dace tun da wuri, domin a yi nasara a 2023, lokacin da za a canja mulkin kasa.

Gwamanonin Filato, Simon Lalong, na Jigawa Mohammed Badaru, na Imo, Hope Uzodinma, na Ekiti, Kayode Fayemi, Na Kebbi, Atiku Bagudu da Ministan Albarkatun man Fetur, Timipre Silva.

Share.

game da Author