Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi

0

Fitaccen malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa shi da mabiyan sa ba su yarda da cika azumi zuwa 30 ba, shine yasa suka yi sallar Idi ranar Laraba maimakon Alhamis da sarkin Musulmi ya sanar.

A jawabin da yayi a filin Idi wanda ya karade shafukan sada zumunta a yanar gizo, Sbehin malamin ya ce don saudi Arabiya bata ga wata ba, bai zama dole ace ba a ganshi a Najeriya ba.

” Lokuttan sallar mu na farilla ba daidai yake da na Saudiya ba saboda haka, don basu ga wata ba, ba za mu bi su. Umarnin Annabi za mu bi ba na Saudiyya ba.

Sarkin Musulmi ya yi sanarwar rashin ganin watan Shawwal ranar Talata, inda ya yi kiraga Musulmai su cika azumi 30. Ayi Sallah Idi kuma ranar Alhamis.

Haka kuma a kasar Saudiyya da wasu kasashe sun sanar da rashin ganin watan Shawwal a Kasashen su da yasa duk za su cika azumi.

Mafi yawan musalmai a kasar nan duk suna cika Azumin su 30, domin yin biyayya ga Sarkin Musulmi, jagorar musulman kasarnan kamar yadda SAW ya umarni a yi.

Ranar Alhamis take Sallah.

Tuni gwamnatin tarayya a Najeriya ta bada hutun kwanakin Laraba da Alhamis domin bukukuwan Sallah.

Share.

game da Author