Dalilin da ya sa muka soke lasisin filayen wasu muka baiwa wasu a Kaduna – El-Rufai

0

Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta soke lasisin mallakr filayen wasu da aka baiwa fili a jihar a baya ta sake rabawa wasu shine don kin gina filayen.

A wata takarda wanda gwamnatin jihar ta fitar, wanda maiba gwamna El-Rufai shawara kan watsa labarai, Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu, gwamnatin jihar ta ce, a dalilin shirin da gwamnati ta fitar na tsara jihar Kaduna da maida ita kasaitacciyar birni, dole ake soke filayen wasu da dama da ba za su iya gina filayen ba a baiwa wasu.

Wannan takarda martani ne gwamnati ta bada ga wata jarida da ta wallafa cewa gwamnatin jihar ta kwace filayen mutane ta raba wa ‘yan uwa da abokan arziki.

” Gwamnati ta kwarbe filayen daga hannun wadanda sun dade da mallakar su amma basu iya gina su, aka baiwa wadanda za su iya gina su cikin dan kankanin lokaci.

” Mafi yawa daga cikin filayen suna cikin gari ne aka barsu ba a gine ba. Amma yanzu an baiwa wadanda za su gine su cikin watanni shida zuwa shekara daya.”

Sanarwar ya ce an rarraba filaye irin haka a yankin Millenium City domin nan ma a gaggauta gina su. Sannan kuma hukuma raba filaye ta jihar ta raba akalla filaye 4,359 zuwa yanzu kuma dukkan su gwamnati ta fi maida hankali ne wajen baiwa ma’aikatan gwamnati.

Share.

game da Author