Zargi: Wani mai amfani da shafin twitter na zargin cewa shanu 50 na wasu makiyayi sun mutu sakamakon gubar da ma’aikatan kungiyar tsaro na Amotekun ko kuma matasa a karamar hukumar Akoko a jihar Ondo suka sanya musu.
Takaddamar da ke gudana tsakanin filani makiyayi da manoma, musamman a yankunan kudancin Najeriya ba sabon labari ba ne. Dangane da wannan batu ne ma wani mai amfani da shafin Twitter da adireshi kamar haka: Sarki(@whatsapping_) ya yi zargin cewa matasan karamar hukumar Akoko ko kuma ma’aikatan kungiyar tabbatar da tsaro ta Amotekun a jihar Ondo sun kashe shanu fiye da 50, mallakar wani makiyayi, bayan da suka ba su guba. Mai amfani da shafin ya kuma yi korafin cewa batun bai bulla a kafofin yada labarai ba.
Daura da hoton da ya bayyana wannan zargi, Sarki(@whatsapping_) mai amfani da shafin na twitter ya yi bayani kamar haka:
“Na wayi gari yau da labarin cewa shanu 50 mallakar wani makiyayi sun ci guba sun mutu a hannun Amotekun/ matasa yarbawa, ranar litini a karamar hukumar Akoko da ke jihar Ondo, sai dai babu wanda ya yi Allah wadai da batun, babu koke-koke a kafofin yada labarai. Babu komai a kafofin sadarwa na internet a sunan hashtag (#). Ba komai.”
Sai dai duk da haka ma’abota shafin twitter sama da dubu guda sun sanya alamar sha’awar labarin wasu 600 kuma sun yada labarin, sannan wasu 300 sun bayana ra’ayoyi mabanbanta dangane da batun a karkashin labarin.
Kungiyar Amotekun din da marubucin ya wallafa wata kungiyar tsaro ce a yankin kudu maso yammacin Najeriya wadda gwamnonin yankin suka kaddamar a shekara ta 2020 a matsayin yunkurin su na shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin. Dan haka wannan zargi ba rikici kadai zai iya janyowa ba, zai iya haddasa husumiya idan har ba<’a yi taka tsan-tsan wajen fayyace lamarin ba.
Tantancewa
Dubawa ta fara da tantance sahihancin hoton ta yin amfani da manhajjar Yandex wadda ta kware wajen gano asalin abubuwan da ake yawan sanyawa a shafin yanar gizo. Sakamakon binciken ya nuna cewa hoton matattun shanun ya yi mafari ne daga wani labarin da ya dauki hankali a shekara ta 2019 lokacin da wata tsawar da aka yi a Oke Owa, a al’ummar Ijare da ke karamar hukumar Ifedore da ke jihar Ondo, ta kashe shanu 36.
An yi ta yada labarin sadda abun ya afku shekaru 3 da suka gabata a kafofin yada labarai daban-daban. Ke nan @sarki ya ba da labarin karya ne kawai a kan hoton.
A Karshe
Hoton da Sarki(@whatsapping_) ya yi amfani da shi a matsayin hujja ga bayanin da ya yi dadadden hoto ne, wanda ya kaga labari a kai dan jan hankalin jama’a.
Discussion about this post