Da gaske ne! Cutar COVID-19 mai nau’in Indiya ta bayyana a Najeriya – Binciken DUBAWA

0

Kwayoyin cuta sun saba rikida a kowani lokaci, inda suke bayyana a nau’o’i daban-daban. Duk da cewa ire-iren wadannan nau’o’in basu da yawa, akwai wadanda ke bazuwa cikin sauki kuma zai yi wahala su ji allurar rigakafi.

Kwayar cutar da ke janyo COVID-19 (SARS-CoV-2) wani nau’i ne na coronavirius, sunan da aka sanyawa dangin kwayoyin cutar da ke da kayoyi a kan su. Wata kungiyar hadin-kan hukumomi na gwamnagtin Amurka ce da kirkiro tsarin da ya kasa na’uo’in cutar COVID-19 zuwa gida uku wadanda suka hada da: Nau’in masu amfani, nau’in masu matsala da nau’in wadanda suke da mtsanancin illa.

Kwanan nan ne wani labari ya bulla a wata taskar blog mai suna Lindaikejiblog official, yana zargin cewa an gano nau’in Indiya na kwayar cutar ta coronavirus a jihohin Edo da Osun a Najeriya. Wannan taskar ta rawaito Farfesa Oyewale Tomori yana bayyana hakan a wata hirar da ya yi da jaridar Leadership.

Da dama sun dauki hoton wannan labarin daga shafin na @lindaikejiblog suna yadawa a manhajjan whatsapp. A nan ne daya daga cikin masu amfani da shafin DUBAWA ya turo mana dan mu tantance gaskiyar labarin.

Tantancewa

DUBAWA Ta fara da duba kalmomin da ake dangantawa da nau’in cutar ta Indiya da yadda ya ke yaduwa dan gano rahotanni masu sahihanci dangane da su.

Shin, da gaske akwai nau’in na Indiya?

Eh akwai nau’in kwayar cutar COVID-19 da aka fi sani da B.1.617 wanda aka fara gani a Indiya a watan Oktobar 2020. Wannan nau’in wanda aka sanya shi cikin rukunin nau’o’i masu matsala a duniya wanda kawo yanzu ya yadu zuwa kasashe 49 a duniya 7 a Afirka a ciki har da Najeriya. Duk wadannan kasashen sun bayana a hukumance cewa sun gano wannan nau’in a kasashensu.

Binciken mahimman kalmomin da muka yi, ya kuma ga rahoton da taskar Lindaikjiblog ta yi amfani da shi, rahoton da jaridar Leadership ta wallafa ranar laraba 12 ga watan Mayu, inda ta ce lallai nau’in kwayar cutar ta shiga Najeriya.

Kuma a rahoton farfesa Tomori ya ba da tabbacin cewa an sami mutane biyar da COVID-19 nau’in Indiya a jihohin Edo da Osun.

Wane ne farfesa Tomori?

Farfesa Oyewale Tomori masanin illimin halitta ne kuma mamba na shirin Global Virome wanda ke binciken cututtuka da samar da sabbin dabaru na tabbatar da kariya daga kamuwa da cututtuka masu hadarin gaske.

Tomori ne tsohon shugaban makarantar kimiyar Najeriya inda yake da kwarewa a fannonin da suka hada da kwayoyin cuta, kariya daga kamuwa da cututtuka, da kuma matakan shawo kan cututtukan.

Tsakanin shekarar 1994 da 2004, Tomori ya yi aiki da Hukumar Lafiya ta Duniya a yankin Afirka, inda ya taka rawa wajen samar da kungiyar Polio na Afirka. Bayan ne ya zama VC a jami’ar Redeemers da ke Najeriya daga 2004 – 2011.

Haka nan kuma, akwai wasu karin rahotannin da suka sake bayar da tabbacin kasancewar wannan nau’in a Najeriya. Wani rahoton da shafin Pulse Nigeria ya wallafa ya, ambato hukumar yaki da cututtuka ta NCDC tana ba da tabbacin cewa makonnin nau’in na Indiya uku yanzu a cikin kasar a yanzu haka.

Akwai wani rahoton kuma daga jaridar Punch wanda ya ce African Centre of Excellence for Genomics and Infectious Diseases, (ACEGID) wato cibiyar da ke binciken kwayoyin halitta da cututtuka masu saurin yaduwa da ke jami’ar Redeemers a Ede jihar Osun ce ta sanar da hukumar yaki da cututtuka ta NCDC cewa akwai nau’in Indiya makonni ukun da suka gabata.

Haka nan kuma cibiyar ta wallafa labarin a shafin twitter inda ta ba da tabbacin afkuwar lamarin, ta kuma yi alkawarin za’a iya samun karin bayani a gidan talbijin na Arise inda shugaban cibiyar, darekta janar Chike Ihekweazu ya yi hira a daya daga cikin shirye-shiryen gidan talbijin.

Daga nan ne DUBAWA ta gano shirin Arise TV morning show (shirin safe) inda hukumar ta NCDC ta yi bayanin yadda ta sami labarin daga ACEGID ganin cewa tana daya daga cikin cibiyoyin da take da hadakar bincike da NCDC.

A cikin bidiyon Ihekweazu ya ce komai na tafiya yadda ya kamata. Ya kuma kara da cewa dokar haramta tafiyar da aka sanya a kan kasashen Indiya da Turkiyya da Brazil makonni biyun da suka gabata, bisa shawarar da hukumar NCDC ta bayar ne.

A Karshe

Hakika nau’in Indiya mai suna B.1.617 ya bulla a Najeriya, makonni uku da suka gabata. Hukumar NCDC ta tabbatar da hakan, amma ta ce komai na tafiya yadda ya kamata. Yayin da sabbin nau’o’i ke bulla, masana kimiya na aiki tukuru dan gano irin hayalen cutar alal misali: yadda cutar ke yaduwa, da yadda ya kan iya janyo cututtuka masu lahani da ma gano ko alluran rigakafin da aka amince da su za su taimaka wajen kare jama’a daga kamuwa da cutar. Duk da haka dai ana cigaba da bayar da shawarar bin ka’idojin da aka gindaya na kare kai daga kamuwa da cutar ta COVID-19.

Share.

game da Author